Dangote Ya Ɗaga Jarinsa a Afrika zuwa $70bn, Zai Inganta Wuta a Najeriya
- Alhaji Aliko Dangote ya ƙara shirin zuba jari a Afirka daga dala biliyan 50 zuwa biliyan 70 wanda hakan zai kawo sauyi
- Attajirin ya bayyana shirin samar da megawatt 10,000 na wutar lantarki a faɗin Afirka, ciki har da Najeriya
- Ya ce ƙarancin wutar lantarki na kawo cikas ga ƙananan masana'antu da matsin tattalin arzikin ƙasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
ABUJA – Attajirin ɗan kasuwa kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana shirin ƙara jarin da ƙungiyarsa za ta zuba a nahiyar Afirka daga dala biliyan 50 zuwa kusan dala biliyan 70.
Dangote ya kuma bayyana shirin samar da megawatt 10,000 na wutar lantarki a faɗin Afirka, wanda Najeriya za ta iya kasancewa cikin ƙasashen da za su amfana da wannan shiri.

Source: UGC
Attajirin ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ya gudanar da masu ruwa da tsaki a masana'antar nishaɗi da kafafen yaɗa labarai daga Arewacin Najeriya, ciki har da 'yan jarida da jaruman Kannywood, cewar Arise TV.
A cewarsa, samar da kayayyaki, buɗe guraben ayyukan yi da tabbatar da wadatacciyar wutar lantarki na daga cikin muhimman abubuwan da za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin Najeriya.
Dangote ya bayyana shirin zuba dala biliyan 70
A cikin wata sanarwa da sashen yaɗa labaran kamfanin Dangote ya fitar ranar Alhamis, attajirin ya ce ƙungiyar na duba yiwuwar ƙara jarin da take shirin zubawa a nahiyar daga dala biliyan 50 zuwa kusan dala biliyan 70.
Ya ce:
"Da farko mun shirya zuba dala biliyan 50. Yanzu muna duba yiwuwar ƙara wannan adadi zuwa kusan dala biliyan 70 a Afirka."
Dangote ya bayyana cewa wannan shiri na cikin manufar kamfanin ta Vision 2030, wadda ke da burin faɗaɗa ayyukan masana'antu da samar da ababen more rayuwa a nahiyar.

Kara karanta wannan
Akume ya ɗauko abin da ya faru a 1999, ya zargi Atiku da yunƙurin karya alƙawari a zaɓen 2027
Ya ƙara da cewa kamfanonin Afirka ya kamata su ɗauki nauyin zuba jari a nahiyarsu tare da taimakawa wajen magance matsalolin ababen more rayuwa da ke hana sauran masu zuba jari shigowa.
Shirin Dangote na samar da megawatt 10,000
Attajirin ya bayyana cewa kamfaninsa na da kusan megawatt 1,500 na wutar lantarki da yake samarwa domin gudanar da ayyukansa.
Sai dai ya ce nan da shekarar 2030, ana sa ran ƙarfin samar da wutar lantarkin zai kai tsakanin megawatt 4,500 zuwa 5,000.
Ya bayyana cewa wannan wutar lantarki za ta ci gaba da kasancewa ta musamman domin bukatun kamfanonin Dangote, cewar Punch.
Baya ga haka, ya ce suna nazarin yiwuwar shiga harkar samar da megawatt 10,000 na wutar lantarki a faɗin Afirka, inda Najeriya za ta iya kasancewa cikin ƙasashen da za su amfana.

Source: Facebook
Ya bayyana yadda ƙarancin wuta ke shafar kasuwanci
Dangote ya bayyana cewa matsalar ƙarancin wutar lantarki na daga cikin manyan ƙalubalen da ke kawo cikas ga ƙananan da matsakaitan masana'antu a Najeriya.
Ya ce kasuwancin da ke dogaro da janaretocin mai da dizal wajen samar da wutar lantarki na fuskantar wahalar samun riba saboda tsadar gudanar da ayyukansu.
Ya bayyana cewa:
"Samar da hasken rana domin amfanin kanka ba yana nufin an magance babbar matsalar ba. Akwai wasu mutane da ba su da wannan damar."
Ya ƙara da cewa ƙananan da matsakaitan masana'antu na taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da tattalin arziki, don haka dole ne a samar musu da yanayin da zai ba su damar bunƙasa.
'Ba a so haka ba'- Dangote kan hannun jari
Mun ba ku labarin cewa Aliko Dangote ya bayyana cewa tayin hannun jarin matatar mansa bai cimma burin jawo masu zuba jari miliyan 10 ba.
ai dai ya ce tayin ya samu gagarumar karɓuwa daga miliyoyin mutane duk da ƙarancin lokacin da aka ba da dama.
Rahoto ya nuna cewa an samu wadanda suka nemi sayen hannun jari ta Naira tiriliyan 6.4, kusan ninki uku na adadin da aka yi niyyar sayarwa.
Asali: Legit.ng

