Uwar Dangote, Mariya Dantata ta ciyar da gajiyayyu 5000, ta gina Masallaci

Uwar Dangote, Mariya Dantata ta ciyar da gajiyayyu 5000, ta gina Masallaci

- Mahaifiyar hamshakin attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, Hajiya Mariya Sunusi Dantata ta gina Masallaci

- Mariya Dantata tana ciyar da Talakawa 5000 a duk rana

Mahaifiyar hamshakin attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, Hajiya Mariya Sunusi Dantata ta kammala ginin wani katafaren masallacin Juma’a a jihar Kano, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta samu labarin ne ta cikin wata sanarwa da aka fitar, inda aka kara da bayyana Mariya na ciyar da sama da mutane gajiyayyu su 5,000 abinci a duk rana.

KU KARANTA: Solomon Dalung ya halarci Tafsirin Sheikh Pantami

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ne ya kaddamar da Masallacin bayan ya jagoranci sallar Juma’a a cikinta, Sarkin ya jinjina ma Hajiya Mariya kan gudunmuwar da take baiwa addinin Musulunci, daga nan ya roki Allah ya saka mata da alheri.

Uwar Dangote, Mariya Dantata ta ciyar da gajiyayyu 5000, ta gina Masallaci
Mariya Dantata tare da Sarkin Kano

A cewar Sarki, gaba daya nahiyar Afirka ta amfana da Hjaiya Mariya, sakamakon haihuwar Aliko Dangote da tayi, shi ma Dangote ya samu halartan kaddamar da Masallacin, haka zalika mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar da sauran manyan gwamnati.

Uwar Dangote, Mariya Dantata ta ciyar da gajiyayyu 5000, ta gina Masallaci
Masallacin

Da take jawabi ga yan jaridu, Mariya tace ta gina wannan Masallaci ne saboda Allah, kuma tace ba zata gaza ba wajen tallafa ma gajiyayyu. Jama’a da dama sun yaba ma Hjaiyar, inda suka ce ta saba gina Masallatai da Asibitoci.

Uwar Dangote, Mariya Dantata ta ciyar da gajiyayyu 5000, ta gina Masallaci
Jama'a a taron Masallacin

Sakamakon halin Hjaiya Mariya na taimakon Al’umma ne ya sanya jami’ar Bayero karramata da shaidar digiri na Dakta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Farashin kayan masarufi a watan Ramadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng