Cikin Sauki: Yadda Opay ke Taimaka Wa Mutane Su Karbi Tallafin Gwamnati na N50,000
- Gwamnatin Tarayya ta bullo da tallafin N50,000 duk wata domin taimaka wa ’yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi da matsin tattalin arziki ya shafa
- Opay na cikn kamfanonin hada-hadr kudi ta intanet da gwamnatin tarayya ta amince da su wajen tura wa wadanda suka cancanta tallafin
- Kamfanin Opay ya bullo da hanyoyi daban daban da suke taimaka wa yan Najeriya wajen karbar wannan tallafi cikin sauki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta bullo da shirin National Emergency Relief and Stabilisation Intervention (NERSI) domin tallafa wa ’yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi da matsalolin tattalin arziki suka shafa.
A karkashin wannan shiri, gwamnatin Najeriya na turawa yan Najeriya da suka cancanta kuma aka zabe su, tallafin N50,000 kowane mutum domin rage mass radadi.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Opay Digital Services na daya daga cikin kamfanonin da Gwamnatin tarayya ta amince da su wajen biyan wannan tallafi.
Kamfanin OPay na taimaka wa shirin ta hanyar samar da ingantacciyar kafar biyan kuɗi ta zamani, wadda masu cin gajiyar tallafin za su iya amfani da ita wajen tantance matsayinsu da karɓar kuɗaɗen da aka ware musu.
Masu amfani da OPay da suka cancanci tallafin za su iya duba matsayinsu kai tsaye ta manhajar OPay ko kuma ta hanyar danna lambar *955*20#.
Sai dai, dan kana da asusun OPay ba ya nufin cewa za a baka tallafin ba, sai dai idan ka samu sakon da ke nuna kana cikin wadanda aka zaba.
Yadda ake duba cancanta ta OPay
Abokan cinikin OPay za su iya tantance ko sun cancanci tallafin ta hanyoyi biyu: manhajar OPay ko lambar USSD.
Ta manhajar OPay, ana son mutun ya buɗe manhajar OPay ta waya, sannan ya duba shafin farko na manhajar domin ganin sanarwar tallafin NERSI na N50,000
Idan an zaɓe mutum, sanarwar za ta bayyana, daga nan sai ya danna sanarwar sannan ya bi umarnin da aka nuna domin ci gaba da karbar tallafin.
Ta lambar USSD kuma, yan Najeriya za su iya amfani da lambar wayar da aka haɗa da asusun OPay, su danna *955*20#, idan mutum na ciki zai gani.
OPay ya jaddada cewa ba shi ke zaɓar waɗanda za su amfana da tallafin ko tantance cancantarsu ba, Gwamnatin Tarayya ce ke da wannan alhakin
Gudunmawar OPay ga shirin NERSI
A matsayinta ɗaya daga cikin abokan hulɗar gwamnati da aka amince da su wajen biyan kuɗin, OPay na taimaka wa ’yan Najeriya da suka cancanta samun tallafin ta hanyar amintaccen tsarin biyan kuɗinta na zamani.
Ya shawarci abokan cinikin OPay da su buɗe manhajarsu domin duba ko sanarwar tallafin NERSI na N50,000 ta bayyana a shafin farko.
Idan mutum ya lura da wani abu da yake zargi ko kuma yana buƙatar ƙarin bayani, zai iya tuntuɓar layin taimakon NERSI ta lambar 0700-022-2222.
Asali: Legit.ng

