EFCC Ta Karbi Korafi da Jerin Kadarori 10 da Ake Zargin Suna da Alaka da Kwankwaso

EFCC Ta Karbi Korafi da Jerin Kadarori 10 da Ake Zargin Suna da Alaka da Kwankwaso

  • Wata ƙungiyar farar hula ta roƙi EFCC ta binciki kadarori 10 da ta ce ana danganta su da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso
  • Ƙungiyar ta nemi a tantance masu kadarorin da kuma tushen kuɗin da aka yi amfani da su wajen sayensu
  • Ta kuma buƙaci a gudanar da binciken kadarorin Kwankwaso, asusun bankunansa da bayanan harajinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Wata ƙungiyar farar hula ta nemi Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta gudanar da bincike kan kadarori 10 da ake zargin suna da alaƙa da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Kungiyar mai suna Society for Anti-Corruption and Good Governance Initiative (SACGGI) ta nemi EFCC ta tantance masu wadannan kadarori da kuma tushen kuɗin da aka yi amfani da su wajen sayensu.

Kara karanta wannan

Abin da muka sani kan batun APC ta rubuta wasika ga INEC don tabbatar da nasarar Tinubu

Kwankwaso.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Leadership ta rahoto cewa SACGGI ta miƙa ƙorafi a hukumance ga hukumar a Abuja ranar Talata, tana mai cewa gudanar da binciken ya zama dole domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana.

Miƙa ƙorafin ya biyo bayan zanga-zangar da mambobin ƙungiyar suka gudanar, inda suka buƙaci EFCC ta gudanar da bincike domin gano ainihin masu kadarorin da kuma tantance ko sayensu ya yi daidai da halastattun kuɗaɗen shigar Kwanakwaso.

EFCC ta karbi korafi kan Kwankwaso

Da yake karɓar ƙorafin a madadin shugaban EFCC, Shugaban Ma’aikatan hukumar, Michael Nzekwe, ya tabbatar wa masu zanga-zangar cewa za a kula da damuwarsu yadda ya kamata.

Ya ce hukumar za ta nazarci ƙorafin bisa hujjojin da ke cikinsa, tare da gudanar da aikin cikin ƙwarewa ba tare da la’akari da matsayin siyasar wanda abin ya shafa ba.

Nzekwe ya ce:

“EFCC ba ta da alaƙa da siyasa. Ba ma goyon bayan wata jam’iyya. A nan muna akki ne kawai domin tabbatar da cika manufofin hukumar. Mun ga abin da kuka gabatar, kuma za mu duba shi bisa cancantarsa tare da gudanar da aikin cikin ƙwarewa.”

Kara karanta wannan

Rashin Imani: Yan bindiga sun rutsa bayin Allah suna barci, sun bude masu wuta

Ya ƙara da cewa za a miƙa ƙorafin ga shugabannin hukumar EFCC domin ɗaukar matakin da ya dace.

Kadarorin 10 da aka nemi a bincika

Da yake magana tun da farko, kakakin ƙungiyar, Muhammad Abdullahi, ya ce SACGGI ta himmatu wajen ƙarfafa riƙon amana a aikin gwamnati da tabbatar da cewa ana bincikar zarge-zargen almundahana ta hanyoyin da suka dace..

Abdullahi ya ce ƙorafin ya lissafa kadarori 10 da ke Abuja, Kano da Jihar Nasarawa, waɗanda ƙungiyar ke ganin ya kamata a gudanar da bincike mai zaman kansa a kansu.

Kadarorin sun haɗa da:

  1. Makarantar Key Science Academy da ke gefen babbar hanyar Abuja zuwa Keffi a Masaka, Jihar Nasarawa
  2. Tsohuwar hedikwatar jam’iyyar NNPP da ke Area 11, Abuja
  3. Gida mai lamba Plot 3060 da ke Maitama, Abuja
  4. Tsohon otal ɗin Clintonia da ke Apo, Abuja
  5. Tidbe Plaza da ke yankin Central Business District, Abuja
  6. Wasu kadarori da ke Garki da Maitama
  7. Makarantar Nigeria-Egypt International School da ke Gwarinpa, Abuja
  8. Kano Mansion da ke Miller Road, Kano
  9. Hafsat Plaza da ke Constitution Avenue, Abuja

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da matar da ake zargin Sarkin Daura ya taɓa jikinta

Kwankwaso ya yi gwamnan Kano daga shekarar 1999 zuwa 2003 da kuma 2011 zuwa 2015. Ya kuma riƙe muƙamin Ministan Tsaro daga 2003 zuwa 2007, sannan ya wakilci Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2019.

Kwankwaso ya soki gwamnatin Tinubu

Kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso , ya nuna damuwa kan ƙara tabarbarewar rashin tsaro, talauci da matsin tattalin arziki da mutanen Arewa maso Gabas ke fuskanta.

Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC ya kuma soki abin da ya kira tara dukiya da wasu jami’an gwamnati ke yi, yayin da talakawa ke ci gaba da fama da talauci

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262