Gwamnatin Katsina Ta Bullo da Sabon Tsari bayan Abin da Ya Faru da Sarkin Daura
- Gwamnatin Katsina ta gindaya sharadin neman izini ga sarakunan gargajiya kafin karɓar baƙi daga ƙasashen waje
- Umarnin ya tanadi neman izini daga sassan kula da ladabi da tsaro na ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina
- Matakin ya zo kwana guda bayan dakatar da harkoki da tafiye-tafiyen Sarkin Daura kan zargin cin zarafin wata ’yar yawon buɗe ido daga ƙasar waje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Gwamnatin Jihar Katsina ta umarci sarakuna da sauran masu riƙe da sarautun gargajiya a jihar da su nemi izinin gwamnati kafin karɓar baƙin ƙasashen waje a fadojinsu.
Umarnin ya tanadi cewa dole ne sarakunan su nemi izini daga sassan kula da ladabi da hulɗa da baƙi da kuma kula da harkokin majalisar zartarwa da tsaro da ke ƙarƙashin ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG) kafin karɓar baƙin ƙasashen waje.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Katsina ta ɗauki mataki kan Sarkin Daura bayan ɓullar bidiyonsa da baturiya

Source: Facebook
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Bala Salisu Zango, ne ya sanar da umarnin a cikin wata sanarwa da ya rattab hannu kuma kakakain gwamnan Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed ya wallafa a Facebook ranar Laraba.
Gwamnatin ta ce an ɗauki matakin ne domin ƙarfafa tsaro, tabbatar da kyakkyawan tsarin gudanar da al’amura da kuma hana karya ƙa’idoji yayin ziyarar baƙin ƙasashen waje ga cibiyoyin sarautun gargajiya.
A cewar sanarwar, an kuma tsara matakin ne domin tabbatar da cewa ana kula da ayyukan sarakuna da suka shafi baƙin ƙasashen waje yadda ya kamata, tare da sanya su ƙarƙashin sa idon gwamnati.
Sanarwar ta bayyana cewa tsarin neman izinin zai bai wa gwamnati damar adana bayanan hulɗar ƙasashen waje da sarakunan gargajiya ke yi, tare da tabbatar da cewa ana tantance irin waɗannan ziyara ta fuskar tsaro.
Zango ya ce umarnin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na ƙarfafa tsaro a matakin ƙananan hukumomi, yana mai cewa sarakuna na ci gaba da kasancewa muhimman abokan hulɗa wajen samar da zaman lafiya a faɗin jihar.

Kara karanta wannan
Atiku ya sake kifar da Tinubu, ya faɗi yadda zai dawo da tallafi, rage farashin fetur
Ya ƙara da cewa gwamnatin Katsina na ganin tattara bayanai da tantance ziyarar baƙin ƙasashen waje zuwa masarautu ya zama dole domin inganta haɗin gwiwa da daidaita harkokin tsaro.
Sanarwar ta zo ne kwana guda bayan da gwamnatin Katsina ta dakatar da dukkan harkokin hukuma da tafiye-tafiyen Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar.
An dauki wannan matakin ne domin gudanar da bincike kan zargin cin zarafin wata mata ’yar yawon buɗe ido daga ƙasar waje da aka yi wa Sarkin Daura.
Kun ji cewa
Asali: Legit.ng