Marasa Lafiya a Asibitocin Abuja na Fuskantar Babbar Matsala bayan Gargadin JOHESU

Marasa Lafiya a Asibitocin Abuja na Fuskantar Babbar Matsala bayan Gargadin JOHESU

  • Ƙungiyar JOHESU ta ba Hukumar FCTA wa’adin kwana bakwai ta aiwatar tare da biyan bashin alawus ɗin ƙwararru ga ma’aikatan lafiya
  • Ta ce ana nuna bambanci wajen biyan alawus, inda ma’aikatan lafiya ƙarƙashin tsarin CONMESS ke amfana, amma aka ware waɗanda ke ƙarƙashin CONHESS
  • Ƙungiyar ta gargaɗi cewa za a iya samun tsaiko a ayyukan kiwon lafiya a Abuja idan ba a warware matsalar ba kafin ranar 23 ga Nuwamba, 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ƙungiyar Ma’aikatan Lafiya ta Haɗin Gwiwa ta Ƙasa (JOHESU), reshen Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, ta yi barazanar shiga yajin aiki.

Kungiyar ta ba da wa’adin kwana bakwai na fara yajin aiki bisa zargin gazawar hukumar gudanarwa ta Abuja (FCTA) wajen aiwatarwa da kuma biyan bashin alawus ɗin ƙwararru da aka amince da shi (PAT).

Kara karanta wannan

Ciyaman a Kano ya ballo ruwa, ya yi barazana ga jama'a kan zaben APC a 2027

Wike.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Source: Twitter

Leadership ta rahoto cewa JOHESU ta yi ikirarin cewa mahukuntan Abuja sun gaza biyan alawus ɗin PAT ga ma’aikatan lafiya ƙarƙashin tsarin albashi na CONHESS.

Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa ayyukan kiwon lafiya a asibitocin da ke faɗin Abuja na iya samun tsaiko idan ba a magance buƙatunta da suka rage ba kafin cikar wa’adin a ranar 23 ga Nuwamba, 2026.

JOHESU, wadda ta ƙunshi Ƙungiyar Ma’aikatan Lafiya ta Najeriya (MHWUN) da Ƙungiyar Ƙwararrun Ma’aikatan Lafiya Masu Alaƙa da Jinya ta Najeriya (NUAHP), ta zargi Hukumar FCTA da nuna bambanci wajen aiwatar da biyan alawus.

Hakan dai na kunshe ne a cikin sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis, wadda shugabanta na reshen Abuja, Kwamared Ene Nwachinerem, da sakatarenta, Kwamared Henry Oshowo, suka sanya wa hannu.

Kungiyar ta ce ta riga ta aika wa hukumar wasiƙar korafi a ranar 7 ga Agusta, 2026. Sai dai ta koka da cewa ba a ɗauki wani mataki mai ma’ana ba duk da shafe watanni uku da miƙa korafin.

Kara karanta wannan

Hukumar INEC ta ɗauki darasi, ta sauya tsarin da za ta yi amfani da shi a zaɓen 2027

A cewar JOHESU, rikicin ya samo asali ne daga abin da ta bayyana a matsayin aiwatar da jadawalin alawus ɗin PAT ga wasu ma’aikata kawai.

Ta ce ma’aikatan lafiya ƙarƙashin tsarin albashin likitoci na CONMESS sun amfana da shirin, yayin da aka ware waɗanda ke ƙarƙashin tsarin CONHESS.

Ƙungiyar ta ce ta sanar da Hukumar FCTA game da wannan bambanci ta hannun Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati, inda ta buƙaci a gaggauta fara biyan alawus ɗin da aka amince da shi ga dukkan ma’aikatan lafiya da suka cancanta.

Saboda haka, ƙungiyar ta ce ta bayar da wa’adin kwana bakwai na fara yajin aiki, bisa matsayar shugabancin ƙungiyar na ƙasa kan batun.

JOHESU ta yi kira ga Ministan Abuja, Nyesom Wike, da ya gaggauta shiga tsakani ta hanyar umartar a fara aiwatar da jadawalin alawus ɗin ga ma’aikatan lafiya da suka cancanta ƙarƙashin tsarin CONHESS, tare da biyan bashin alawus da ake binsu.

Halin da yajin aiki ke jema marasa lafiya

Kun ji cewa yajin aikin kungiyar likitoci ta NARD ya fara jefa mutane marasa lafiya cikin wahala musamman masu karamin karfi

Rahoto ya nuna cewa mutane sun fara karkata zuwa asibitocin kudi domin samun kulawa amma suna kuka kan tsadar kudin jinya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262