Gwamnatin Tinubu Ta Gano Dabarun 'Yan Kasuwa, Za a Kawo Karshen Kauce wa Biyan Haraji

Gwamnatin Tinubu Ta Gano Dabarun 'Yan Kasuwa, Za a Kawo Karshen Kauce wa Biyan Haraji

  • Gwamnatin tarayya na shirin kafa cibiyar sa ido kan mu'amalar kuɗin manyan kamfanonin ƙasashen waje da suke saba wa doka
  • Ana so a hana kowa kauce wa biyan haraji ta hanyar karkatar da ribar da kamfanoni suka samu zuwa zuwa ƙasashen masu saukin haraji
  • Hukumar Tara Haraji ta Najeriya (NRS) ta kuma ce tana shirin amfani da fasahar AI wajen gano anihin kudin kaya da aka shigo da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin kafa Cibiyar Nazarin Farashin Kaya ta Ƙasa da nufin yaƙar dabarar da ‘yan kasuwa suke yi.

Manufar ƙirƙiro cibiyar ita ce ta sanya ido kan kamfanonin ƙasashen waje da kuma daƙile karkatar da ribar kasuwanci da ake yi zuwa ƙetare.

Bola Tinubu
Bola Tinubu da wasu shugabannin duniya a taron G20 a kasar waje Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gwamnati ta fahimci ana gudun biyan haraji

Mista Idris Abdullahi, shugaban sashen yaƙi da cin hanci da rashawa da hulɗa da hukumomin tsaro na NRS ya shaida haka in ji The Cable.

Kara karanta wannan

2027: Sanatan Kano ya faɗawa Tinubu gaskiya kan ƙalubalen da APC za ta fuskanta a Arewa

Jami’in Hukumar Tara Kuɗin Shiga ta Ƙasan ya bayyana hakan a ranar Talata, yayin wani taro na horas da 'yan jarida da aka shirya.

An shirya wa ‘yan jarida horo game da yadda za su riƙa yin bincike mai inganci kan fitar da kuɗin haramun da ake yi daga Najeriya.

Yake cewa karkatar da riba zuwa ƙasar waje wata dabara ce da kamfanonin ƙasa da ƙasa ke amfani da ita wajen kaucewa biyan haraji a nan.

Wasu ‘yan kasuwa suna ɗauke ribarsu zuwa ƙasashen da ba a biyan haraji sosai ko kuwa aƙalla ba a damu da tatsarsu kamar Najeriya ba.

Idris Abdullahi ya ce hukumarsu tana aiki tare da Gwamnatin tarayya wajen samar da fasahar AI da za ta riƙa sa ido kan kuɗin da suke fita.

Najeriya ta gano alamar tambaya a wasu ciniki

Jami'in ya ce wani somin-tabin bincike ya nuna tsakanin 2020 da 2024, kwastam ta samu gibin N53.9trn wajen kuɗin kayan da ake shigo da su.

Kara karanta wannan

Shettima ya sanar da shirin raba miliyoyin buhunan taki ga masu noman rani

Ya ce binciken ya yi amfani da tsarin tantance farashi na Majalisar Ɗinkin Duniya kan Cinikayya (UNCTAD) domin gano wata cuwa-cuwa.

Sai dai Abdullahi ya yi ƙarin haske cewa adadin bai nufin an tabbatar da zamba, aikata ba daidai ba ko kuma cewa tiriliyoyin kuɗin sun yi ƙafa.

Gwamnati za ta yi amfani da fasahar AI

The Nation ta rahoto shi yana cewa hasashe ne kawai aka yi kuma don haka za a rungumi fasahar AI domin a magance wata matsala nan gaba.

Abdullahi ya ce Gwamnatin tarayya za ta ƙara dogaro da tattaro bayanai, fasahar AI, tantance kamfanoni da mutane da nazarin cinikayya.

Nan gaba kuma za a dage wajen ganin an hango matsaloli tun kafin su faru saboda gudun Najeriya ta rika asarar kuɗin da ya dace su shiga lalita.

Gwamnati tana kuma shirin inganta yadda ake tantance farashin kayayyakin da ake shigo da su, a koma amfani da farashin kasuwannin duniya.

Bola Tinubu
Jami'an gwamnatin Tinubu ana taro a Abuja da wasu wakilai daga kasar Sin Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gwamnati za ta kara yawan jami'an tsaro

Ana da labari cewa matasa za su samu abin yi idan aka dauki sojoji 28,000 da ’yan sanda 50,000 aiki a kokarin ganin an kawo tsaro.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Gobara ta kama a katafariyar ma'ajiyar babban dan kasuwa a jihar Kaduna

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da ɗaukar sababbin dakaru domin ƙarfafa tsaron ƙasa da rage zaman banza da ake fama da shi.

An kuma fahimci cewa sojoji sun kashe 'yan ta'adda sama da 15,000 yayin da mayakan Boko Haram sama da 130,000 da iyalansu suka tuba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng