Abin Tausayi: Matashi Ya Mutu a Kokarin Kare Iyayensa daga Sharrin Yan Bindiga

Abin Tausayi: Matashi Ya Mutu a Kokarin Kare Iyayensa daga Sharrin Yan Bindiga

  • Yan bindiga kusan su bakwai sun kai hari gidan wani mutum mai shekaru 70 a ƙauyen Nabai Fulani da ke ƙaramar hukumar Garki a jihar Jigawa
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun harbe Lawan Yahaya mai shekaru kusan 30 har lahira lokacin da yake ƙoƙarin kare iyayensa
  • Yan bindigar sun tsere da babur kirar Boxer mai launin ja da kuɗi da ba a bayyana adadinsu ba amma ba su tafi da kowa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigawa, Nigeria - ’Yan bindiga sun kashe wani matashi mai shekaru 30 tare da jikkata iyayensa a wani harin tsakar dare da suka kai gidansu a ƙauyen Nabai Fulani, da ke unguwar Kargo a ƙaramar hukumar Garki ta jihar Jigawa.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:50 na safiyar Litinin, 16 ga Nuwamban 2026, lokacin da yan bindigar su kusan bakwai ɗauke da makamai suka kutsa cikin gidan wani mutum mai shekaru 70, mai suna Yahaya Jibrin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake barna a Zamfara bayan kashe hadimin Gwamna Dauda

Jigawa.
Taswirar jihar Jigawa da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Leadership ta ruwaito cewa jami’in hulɗa da jama’a na rundunar tsaro ta farin kaya (NSCDC) reshen jihar Jigawa, ASC Badaruddeen Tijjani, ya tabbatar da harin cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Dutse ranar Talata.

Yadda mahara suka kashe matashi

A cewar Tijjani, maharan da ake zargin ’yan fashi da makami ne, sun kutsa cikin gidan tare da farmakar Jibrin da matarsa mai shekaru 45, Zainab Yahaya.

Rahotanni sun ce yan bindigan harbe ɗansu, Lawan Yahaya, mai kimanin shekaru 30, har lahira lokacin da ya yi ƙoƙarin ceton iyayensa.

“Bayanan farko sun nuna cewa waɗanda ake zargin suna ɗauke da bindigogin AK-47,” in ji kakakin NSCDC.

Ya ƙara da cewa maharan sun tsere da babur kirar Boxer mai launin ja, wanda ba shi da lambar rajista, da kuma kuɗi da ba a bayyana adadinsu ba.

Tijjani ya ce jami’an rundunar ’yan sandan sashen Garki sun dauke gawar mamacin zuwa asibitin, inda wani likita ya tabbatar da rasuwarsa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta fadi karyar da ta ce an shirya kan kai wa Kwankwaso hari

Daga bisani, an miƙa gawar ga iyalansa domin gudanar da jana’izarsa bisa tsarin addinin Musulunci, kamar yadda Aminiya ta rahoto.

Hukumar NSCDC ta yi Allah wadai

Kakakin NSCDC ya bayyana cewa kwamandan rundunar na jihar, CC Kabiru Ingawa, ya yi Allah-wadai da harin tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin.

Jami'an NSCDC.
Jami'an hukumar tsaro ta NSCDC a bakin aiki Hoto: @OfficialNSCDC
Source: Facebook

Kwamandan ya kuma tabbatar wa mazauna yankin cewa rundunar za ta ci gaba da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin ƙarfafa tsaro, kare rayuka da dukiyoyi.

Tijjani ya kuma roƙi jama’a da su bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wa hukumomin tsaro wajen gano waɗanda ake zargin da kuma kama su.

Yan bindiga sun sace mutane 12

Kun ji cewa mahara da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari ƙauyen Kurmin Wali da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna, inda suka sace mutum 12.

Daga cikin waɗanda aka sace, mutum uku sun tsere sun koma gida, yayin da tara ke hannun masu garkuwa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262