Tsugunne ba Ta Kare ba, Kotu Ta Dauki Mataki kan Matsalar Auren Gwamna Abba

Tsugunne ba Ta Kare ba, Kotu Ta Dauki Mataki kan Matsalar Auren Gwamna Abba

  • Babbar Kotu da ke Abuja ta sanya ranar 15 ga Disamba domin ci gaba da sauraron ƙarar neman saki da Zainab Kwankwaso ta shigar
  • Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kano, Sanusi Bature, ya halarci zaman kotun a madadin gwamna, inda ya tabbatar da karɓar takardun ƙarar
  • Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da matsalar aurensa a bainar jama’a, inda ya ce ya amince ya zauna da mata ɗaya a yanzu, amma yana iya sake aure nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Wata kotun Upper Area Court da ke Abuja ta sanya ranar 15 ga Disamba domin ci gaba da sauraron ƙarar neman saki da Zainab Kwankwaso, matar Gwamnan Kano, Abba Yusuf, ta shigar.

An saurari ƙarar mai lamba CV/97/26 ne a ranar Talata, 17 ga watan Nuwamban 2026 a gaban mai shari’a Ado Muktar.

Kara karanta wannan

Malamin Musulunci ya sha kaye a ƙokarinsa na samun tikitin takarar gwamnan Kano a 2027

An fara zama kan batun auren Gwamna Abba
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jawabi a wajen taron bayar da tallafi Hoto: Isah Muhammad Salisu
Source: Facebook

Kwamishinan Abba ya halarci zaman kotu

A yayin zaman kotun, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Sanusi Bature, ya bayyana a madadin gwamnan, inda ya sanar da kotun cewa ya karɓi takardun ƙarar a madadinsa, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Sanusi Bature ya kuma miƙa wa kotun wata takarda domin amfani da ita yayin gudanar da shari’ar.

Ya bayyana cewa akwai batutuwa biyu da suka shafi lamarin, inda ya ce ɗaya daga cikinsu yana gaban kotu, yayin da ɗayan kuma batu ne na cikin gida da ya shafi iyali.

Kwamishinan ya buƙaci ’yan jarida su yi taka-tsantsan tare da tabbatar da tsaka-tsaki wajen yaɗa labarin, yana mai jaddada cewa ya kamata a mutunta yanayin sirrin lamarin.

Lauyan mai shigar da ƙarar, Aliyu Baba, shi ma ya halarci zaman kotun.

Abba ya tabbatar da matsalar aurensa

A ranar Litinin, gwamnan ya fito fili ya tabbatar da matsalar aurensa da Zainab Musa Kwankwaso, ’yar’uwar tsohon jagoransa a siyasa, Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Abin jimami: Gobara ta lakume ango da amarya suna cikin barci

Kwankwaso ne ya raini Zainab, kuma mutane da dama suna kallonsa a matsayin mahaifinta.

Gwamnan ya bayyana batun ne cikin raha yayin da yake jawabi ga ’yan fansho a gidan gwamnatin Kano ranar Litinin.

Gwamna ya ce zai iya kara aure nan gaba

Duk da haka, Abba Kabir Yusuf ya nuna cewa yana iya sake yin aure a nan gaba.

"Amma ku sani, zan ƙara aure nan gaba. Wasunku ba za su fahimci abin da gwamna yake nufi da wannan magana ba.” In ji shi.

Gwamnan ya kuma yi maganar da ta nuna cewa an riga an kammala matakin sakin auren, inda ya ce an fitar da takardar sanar da rushe auren.

Abba Kabir Yusuf ya kuma roƙi al’ummar Kano su yi masa addu’ar samun matar da ta dace da shi, yana mai cewa ya gamsu da matakin da aka ɗauka tare da roƙon Allah ya shiryar da shi zuwa ga mutanen kirki.

Abba ya yi magana kan aurenaa
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jawabi a wajen taro Hoto: Isah Muhammad Salisu
Source: Facebook

Dalung ya yi magana kan auren Gwamna Abba

Kara karanta wannan

Sabon tsarin da Kwankwaso yake so a yi amfani da shi a zaben shugaban kasa a Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mnistan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya yi magana kan batun rabuwar auren Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da matarsa, inda ya soki yadda gwamnan ya bayyana matakin da ya dauka.

Dalung ya ce ba ya adawa da shawarar Abba ta kawo karshen aurensa idan hakan ne yake so da gaske, amma ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda aka gudanar da lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng