Guna Guni Sun Yi Yawa, Tinubu Ya Wayar da Kan Yan Kasa kan Rancen N100m
- Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirin MREIF da zai bai wa ’yan Najeriya damar karɓar bashin sayen gida har Naira miliyan 100
- Shirin zai ba masu cin gajiyarsa damar biyan bashin cikin shekaru 20, da ribar kashi 9.75 cikin 100 a shekara
- Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ta ji korafe-korafen jama’a, inda ya fitar da bidiyo domin amsa tambayoyinsu kan shirin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da wani shirin bayar da bashin kuɗin sayen gidaje wanda zai bai wa ’yan Najeriya damar karɓar har Naira miliyan 100 domin mallakar gidajensu.
Shugaba Tinubu ne ya bayyana shirin mai suna MREIF da ke cikin tsare-tsaren gwamnatinsa na taimaka wa ’yan Najeriya wajen samun gidajen kansu.

Source: Facebook
Wadanda za su ci gajiyar shirin

Kara karanta wannan
Rikicin APC a jihar Kano ya yi ƙamari, an aika saƙon gaggawa ga Tinubu da Abdulaziz Yari
Jaridar Punch ta ruwaito cewa shirin zai bai wa masu neman rancen damar karɓar kuɗin ne da ribar kashi 9.75 cikin 100 a shekara.
Haka kuma, an tanadi wa waɗanda suka ci gajiyar shirin damar biyan bashin cikin wa'adin shekaru 20.
A cewar bayanin da shugaban ƙasar ya yi, mutum zai iya samun bashin ne bayan ya biya kashi 10 cikin 100 na kuɗin gidan da yake son saya a matsayin kuɗin farko.
Misali, idan mutum ya zaɓi gida mai darajar Naira miliyan 10, abin da ake buƙata shi ne ya fara biyan Naira miliyan ɗaya, yayin da zai samu damar biyan ragowar kuɗin a hankali bisa tsarin da aka tanada.

Source: Facebook
Korafe-korafen yan Najeriya kan rancen
Yan Najeriya da dama sun yi ta korafi, tambayoyi da kuma korafe-korafe game da rancen da aka shirya bayarwa.
Hakan bai da nasaba da rudani da ke cikin rancen wanda ya tilasta yan kasa ke neman bahasi domin samun cikakken bayani.
Shugaba Bola Tinubu da kansa ya duba korafe-korafen al'umma inda ya yi martani game da shirin a shafin X

Kara karanta wannan
An ba 'yar Amurka Dala miliyan 4.5 bayan ta yi hira da Shugaba Tinubu? Gaskiya ta bayyana
Tinubu ya kwantar wa yan kasar hankali inda ya wayar masu da kawuna wurin yada bidiyo kan shirin.
A cikin sanarwar, Tinubu ya ce:
"Ya ku ƴan Najeriya,
"Mun ji ra’ayoyinku da korafe-korafen da kuka bayyana.
"Ku kalli wannan bidiyo domin samun amsoshin tambayoyinku game da shirye-shiryen bayar da rancen kuɗin sayen gidaje da kuma samar da gidajen araha ga al’umma....Bola Ahmed Tinubu, GCFR."
Yadda za a samu tallafin N100
Mun ba ku labarin cewa shirin NFSP na bayar da tallafin Naira 100,000 ga iyalai matalauta da masu rauni, domin rage musu nauyin tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki.
Gwamnati na amfani da National Social Safety Net System da lambar NIN wajen tantance masu cancanta da kuma kauce wa maimaita sunayen masu cin gajiyar shirin.
Masu sha’awar shiga shirin za su iya yin rajista ta shafin intanet da aka samar, amma cika fom ba ya tabbatar da samun tallafin kai tsaye.
Asali: Legit.ng