Takarar Atiku: ADC Ta Dauki Mataki domin Maganin Nafiu Bala
- Jam’iyyar ADC ta shigar da ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara, tana ƙalubalantar hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke kan shugabancinta
- Jam’iyyar ta bukaci kotun ta hana INEC sauya bayanan shugabanninta da na ’yan takarar shugaban kasa da gwamnoninta har sai an kammala sauraron ƙarar
- ADC ta ce hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu ya yanke a ranar 5 ga Nuwamba, 2026, na da kura-kurai masu yawa, kuma kotun ba ta da hurumin sauraron karar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jam’iyyar ADC ta shigar da ƙara mai korafe-korafe 17 a Kotun Ɗaukaka Ƙara, inda take ƙalubalantar hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya jefa shugabancinta da shirye-shiryenta na zaɓen 2027 cikin sabon rikici.
Jam’iyyar ta kuma nemi kotun ta hana Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) sauya bayanan shugabancinta da na ’yan takararta har sai an kammala sauraron ƙarar.

Source: Facebook
Punch ta rahoto cewa daraktan sadarwa na dabaru na kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC, Phrank Shaibu, ne ya fitar da sanarwar a ranar Talata.
Korafin da ADC ta mika kotu
ADC ta ce ƙarar da ta shigar na ƙalubalantar tushen hukuncin kotun, tare da nuna cewa Babbar Kotun Tarayya ba ta da hurumin sauraron takaddamar shugabancin jam’iyyar.
Shaibu ya bayyana cewa daga cikin batutuwan da ƙarar ta ƙunsa akwai ko Nafiu Bala Gombe yana da hurumin shigar da ƙarar, yadda kotun ta tantance hujjojin da aka gabatar da kuma umarnin da ta bayar kan jam’iyyar.
Vanguard ta rahoto ya ce:
“Dalilai 17 na ƙarar suna ƙalubalantar tushen hukuncin Mai Shari’a Lifu, abubuwan da ya gano da kuma umarnin da ya bayar.
"ADC ta nemi Kotun Ɗaukaka Ƙara ta duba ko kotun farko tana da hurumin sauraron ƙarar, ko wanda ya shigar da ita yana da matsayi na yin hakan, ko an tantance hujjojin da ake takaddama a kansu yadda ya kamata, da kuma ko umarnin da aka bayar kan jam’iyyar sun dace da doka.”
Bukatar ADC a kotu
ADC ta nuna damuwa kan yiwuwar INEC ta aiwatar da hukuncin ranar 5 ga Nuwamba kafin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke hukunci kan ƙalubalen da ta gabatar.
Ta ce hakan na iya jefa ’yan takararta cikin rashin tabbas, tare da haifar da matsalar da za ta yi wahala a gyara idan Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke hukuncin daga baya.
Shaibu ya ce:
“Dole ne INEC ta guji yin sauye-sauyen da za su iya riga kotu yanke hukunci ko jefa ’yan takarar jam’iyyar cikin matsala yayin da bukatunmu ke gaban kotu. Muna neman kotu ta kare abin da ake takaddama a kai, domin hukuncin da za ta yanke daga baya ya kasance mai tasiri.”

Source: Facebook
Kiran Nafiu Bala ga INEC
A wani labarin, mun rahoto cewa Hon. Nafiu Bala Gombe ya sanar da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) cewa ya koma kan kujerar shugaban jam’iyyar ADC ta ƙasa.

Kara karanta wannan
Akume ya ɗauko abin da ya faru a 1999, ya zargi Atiku da yunƙurin karya alƙawari a zaɓen 2027
Hakan na zuwa ne bayan hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yanke a ranar 5 ga Nuwamba, 2026.
A cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 16 ga Nuwamba, 2026, wadda INEC ta karɓa a wannan rana, Gombe ya sanar da hukumar cewa ya koma bakin aiki bisa hukuncin kotun.
Asali: Legit.ng

