Dr. Aliyu Modibbo Umar ya koma Jam’iyyar APC

Dr. Aliyu Modibbo Umar ya koma Jam’iyyar APC

- Tsohon ministan birnin tarayya Dr Aliyu Modibbo ya shiga Jam’iyyar APC

- Dr. Modibbo ya karbi katin zama dan APC a garin Akko da ke Jihar Gombe

- Tsohon Ministan yace yanzu ganin damar sa ce ta sa ya shiga Jam’iyyar

Dr. Aliyu Modibbo Umar ya koma Jam’iyyar APC

 

 

 

 

 

 

 

 

Tsohon Ministan Kasar nan Dr. Aliyu Modibbo ya shiga Jam’iyyar APC mai mulkin Kasar nan. Dr. Modibbo ya karbi katin sa na zama dan Jam’iyya a gidan su da ke Unguwar Kumo a Karamar Hukumar Akko na Jihar Gombe.

Dr. Modibbo ya zanta da ‘Yan Gidan Jaridar Daily Trust cewa yaga ya dace ya taimakawa Shugaba Muhammadu Buhari wajen ganin Kasar nan ta cigaba. Dr. Aliyu Modibbo yace bai taba shiga wata Jam’iyya ba tun da ya ke. Yace ko can baya da yake Gwamnati, ba wata Jam’iyya ke aika sa ba, don yana cikin ma’aikatan Gwamnati.

KU KARANTA: Rikicin Ganduje da Kwankwasiyya a Kano

Dr. Aliyu Modibbo ya fara Minista tun shekaru kusan goma sha biyar da suka wuce, ya rike Ministan Kasuwancu, sannan kuma ya rike Ministan Birnin Tarayya lokacin Shugaban Kasa Ummaru ‘Yaradua.

Dr. Aliyu Modibbo yake cewa yanzu ya gay a dace ya shiga wata Jam’iyya ta ganin damar sa, domin ya bada ta sa gudumuwar, yace kuma Jam’iyyar APC ce ta fi dacewa da shi

 

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng