Jonathan Ya Fito da Sabuwar Magana kan Dalilinsa na Mika Mulki ga Buhari cikin Sauki

Jonathan Ya Fito da Sabuwar Magana kan Dalilinsa na Mika Mulki ga Buhari cikin Sauki

  • Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana dalilin da ya sa ya miƙa mulki ga Muhammadu Buhari cikin lumana
  • Jonathan ya bayyana hakan ne ta bakin tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Anyim Pius Anyim, yayin bikin ƙaddamar da tarihin rayuwar Buhari a Abuja
  • Kashim Shettima ya yaba wa Buhari, yana mai cewa halayensa sun nuna cewa mutuncin shugabanci yana dogara ne da nagartar wanda ke riƙe da muƙamin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Goodluck Jonathan, ya bayyana dalilin da ya sa ya miƙa mulki ga marigayi Muhammadu Buhari ba tare da wata takaddama ba bayan zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2015.

Jonathan ya ce ya san Buhari a matsayin ɗan kishin ƙasa da ke tsoron Allah, wanda yake matuƙar son ganin Najeriya ta ci gaba.

Kara karanta wannan

APC ta bayyana gaskiyar da ta yarda da ita kan matsalar rashin tsaro a gwamnatin Tinubu

Jonathan ya yi magana kan Buhari
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamban 2026 a Abuja, yayin bikin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar Buhari mai suna “Muhammadu Buhari: The Authorised Presidential Biography”, cewar rahoton jaridar Vanguard.

An rubuta littafin mai juzu’i uku ne ƙarƙashin jagorancin Dakta Udu Yakubu.

Abin da ya sa Jonathan ya amince da mika mulki

Tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Anyim Pius Anyim, wanda ya wakilci Jonathan a wajen taron, shi ne ya bayyana saƙon tsohon shugaban ƙasar.

Anyim ya ce Jonathan ya kira shi ta waya kusan sa'o'i biyu kafin fara taron, inda ya sanar da shi cewa ba zai samu damar halarta ba.

Ya ƙara da cewa Jonathan ya soke dukkan sauran shirye-shiryensa domin tabbatar da cewa an wakilce shi yadda ya kamata a wajen bikin.

A cewarsa, har yanzu wasu ’yan Najeriya na mamakin dalilin da ya sa Jonathan ya amince da sakamakon zaɓen, ya kuma miƙa mulki ba tare da ƙalubale ba.

Kara karanta wannan

"Tinubu ya fi Buhari kokari"; Tsohon gwamna ya kawo dalili

Anyim ya ce Buhari ya shahara a matsayin ɗan siyasar da ya samu nasarar kayar da shugaban ƙasa mai ci, yayin da Jonathan kuma ya yi fice saboda yadda ya miƙa mulki cikin lumana.

Ya bayyana cewa Jonathan ya amince da mika mulkin ne saboda ya yi imanin Buhari mutum ne mai kishin ƙasa.

“Shugaba Buhari ya shahara a matsayin ɗan siyasar da ya iya kayar da shugaban ƙasa mai ci. Shi kuma Shugaba Goodluck ya shahara a matsayin shugaban ƙasa a Afirka da ya miƙa mulki ba tare da wata takaddama ba.
“Abu ne mai sauƙi ga Shugaba Goodluck ya ce, ga wani ɗan ƙasa nagari da na sani, wanda yake son Najeriya. Saboda haka, babu buƙatar wata takaddama. Wannan shi ne dalilin.”

Anyim ya bayyana kusancinsa da Buhari

Tsohon shugaban Majalisar Dattawan ya ce dangantakarsa da Buhari ta samo asali ne tun shekarar 2003, kuma ta ƙara ƙarfi a tsawon lokaci.

Ya bayyana cewa daga baya dangantakarsu ta koma kamar ta uba da ɗa. Anyim ya ce Buhari ya ci gaba da nuna masa wannan kulawa ko bayan ya shiga gwamnatin Jonathan, a lokacin da Buhari yake cikin ’yan adawa.

Kara karanta wannan

Tsohon na kusa da Atiku ya zayyano matsalolin dan takarar na ADC a 2027

"Duk da cewa yana cikin ’yan adawa, ya kan ɗauki lokaci ya kawo min ziyara.” In ji shi.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Jonathan ta riƙa girmama Buhari tare da ba shi dukkan kulawar da ta dace da matsayinsa na ɗan ƙasa nagari.

Shettima ya yaba wa Buhari

A nasa jawabin, mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda Dakta Aliyu Modibbo Umar, mai ba da shawara na musamman kan harkokin gudanarwa a ofishinsa, ya wakilta, ya bayyana Buhari a matsayin mutum na musamman.

Shettima ya ce Buhari mutum ne da ya karya tsarin siyasar da aka saba gani a Najeriya. Ya ce Buhari ya koya masa cewa mutuncin muƙamin gwamnati yana dogara ne da halayen wanda ke riƙe da shi.

A cewarsa, kyakkyawan misalin da shugaba ya bayar yana ci gaba da zama abin tunawa ko bayan ya bar muƙaminsa.

Jonathan ya yabi marigayi Buhari
Goodluck Jonathan na gabatar da jawabi a wajen taro Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Twitter

Jonathan ya nuna damuwa kan zaben 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya nuna damuwa kan alkiblar da Najeriya ke bi gabanin babban zaɓen 2027.

Jonathan ya yi gargaɗin cewa ƙaruwar rashin haƙurin siyasa, tashin hankali da hamayyar ƙabilanci na iya yin barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng