Sabon Littafi Ya Fito kan Buhari, an Fadi Komai daga Yarinta zuwa Rasuwarsa
- An shirya gabatar da sabon littafin tarihin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ga jama’a a Abuja ranar 19 ga Nuwamba
- Littafin mai juzu’i uku ya kunshi tarihin rayuwarsa, aikin soja, gwagwarmayar siyasa da shekaru takwas da ya yi yana mulkin Najeriya
- Mawallafin littafin, Udo Yakubu, ya ce ya shafe sama da shekaru biyu yana gudanar da bincike, tattaunawa da tantance bayanai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – An shirya gabatar da wani sabon littafi mai kunshe da tarihin rayuwar marigayi tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ga jama’a a ranar 19 ga Nuwamba, 2026, a Abuja.
Littafin ya kunshi juzu’i uku, inda aka yi bayani kan rayuwar Buhari, aikinsa na soja, tafiyarsa a siyasa da kuma mulkinsa na tsawon shekaru takwas.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa masanin bincike kuma marubucin littafin, Udo Yakubu, ne ya rubuta shi, yayin da kamfanin May Publishing Limited ya wallafa shi.
Abin da littafin Buhari ya kunsa
Da yake jawabi a taron manema labarai ranar Laraba gabanin gabatar da littafin, Yakubu ya ce ya shafe sama da shekara biyu yana bincike, tattaunawa da mutane, rubutu da kuma tantance bayanai.
Ya bayyana cewa littafin ya bi diddigin rayuwar Buhari tun daga yarintarsa a Daura ta jihar Katsina, zuwa aikin soja, shiga siyasa da kuma zama shugaban kasa a shekarar 2015.
Buhari ya taba zama shugaban mulkin soja daga shekarar 1983 zuwa 1985, kafin ya koma siyasa, inda daga bisani ya lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2015.
Ya yi wa’adi biyu a matsayin shugaban kasa, inda ya kammala mulkinsa a shekarar 2023 kafin Allah ya karbi yaruwarsa a shekarar 2025.
Bayanin da aka yi littafin

Kara karanta wannan
Tsohon shugaban NNPCL ya yi maganar Naira Tiriliyan 210 da ya ‘bace’ lokacin yana ofis
An raba littafin zuwa juzu’i uku, inda juzu’i na farko mai suna ya yi bayani kan asalin gidansu, yarintarsa, aikin soja, rawar da ya taka a yakin basasa, tsare shi da kuma gwagwarmayarsa ta siyasa kafin ya zama shugaban kasa.
Juzu’i na biyu mai suna ya mayar da hankali kan mulkinsa tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023. Ya kunshi muhimman shawarwarin da gwamnatinsa ta yanke, mutanen da suka taka rawa, kalubale da rikice-rikicen da suka dabaibaye mulkinsa.
Juzu’i na uku ya yi nazari kan gadon da Buhari ya bari a fannoni kamar tsaro, tattalin arziki, abubuwan more rayuwa, yaki da cin hanci da rashawa, shugabanci, huldar kasashen waje da hadin kan kasa.

Source: UGC
Yakubu ya ce duk da cewa Buhari ya amince da rubuta tarihin, hakan bai hana shi gudanar da aikin cikin ’yanci a matsayin marubucin tarihin ba.
Shettima ya soki Amaechi kan Buhari
A wani labarin, mun ruwaito cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya soki Rotimi Amaechi, kan zargin da ya yi cewa marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari kan zaben 2023.
Shettima ya bayyana kalaman Amaechi a matsayin rashin girmamawa ga marigayin, wanda ya ce har yanzu yana daga cikin fitattun ’yan siyasar Arewa da ake girmamawa.
Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan magana ne a ranar Talata yayin gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na APC a Dutse, jihar Jigawa.
Asali: Legit.ng
