Moniepoint Ya Fitar da Hanya Mai Sauki Ta Duba Wadanda Za Su Samu Tallafin N50,000

Moniepoint Ya Fitar da Hanya Mai Sauki Ta Duba Wadanda Za Su Samu Tallafin N50,000

  • Kamfanin hada-hadar kudi na Moniepoint ya yi bayani kan yadda mutane za su duba cancantarsu ta karbar tallafin N50,000 daga gwamnatin tarayya
  • Waɗanda aka tabbatar sun cancanta za su iya karɓar kuɗin kai tsaye a asusun Moniepoint ba tare da ƙarin cajin kudi ba
  • Bankin na intanet ya buƙaci abokan huldarsa su yi amfani da lambar USSD wajen tantance cancantarsu da karɓar tallafin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Kamfanin hada-hadar kudi ta intanet, Moniepoint Microfinance ya bayyana cewa abokan huldarsa da aka zaba za su samu tallafin N50,000 daga gwamnatin tarayya

Ya ce mutane za su iya tantance matsayinsu da kuma samun tallafin gaggawa na N50,000 na Gwamnatin Tarayya ta hanyar danna lambobin USSD a wayoyinsu.

Moniepoint.
Tambarin kamfanin hada-hadar kudi ta intanet watau Moniepoint Hoto: Moniepoint
Source: UGC

Moniepoint ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamba, 2026, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Opay, Moniepoint da bankuna 5 da ke tura tallafin N50,000 a Najeriya

Bankin na intanet ya ce waɗanda aka tabbatar sun cancanta za a jagorance su kan matakan amincewa da tallafin, domin a tura kuɗin kai tsaye zuwa asusunsu na Moniepoint ba tare da ƙarin kuɗin caji ba.

Ma’aikatar Jinƙai da Rage Talauci ta Tarayya ce ke jagorantar shirin mai suna NERSI, wanda aka tsara domin bai wa masu karamin karfi taimakon kuɗi kai tsaye don su iya biyan buƙatunsu na yau da kullum.

Moniepoint ya ce yana cikin kamfanonin hada-hadar kuɗi da Gwamnatin Tarayya ta zaɓa domin taimakawa wajen raba kuɗin tallafin.

Sako ga masu amafani da Moniepoint

Babatunde Olofin, shugaban kamfanin Moniepoint ya ce bankin na farin cikin taimaka wa mutanen da suka cancanta wajen samun tallafin da ke ƙarƙashin shirin gwamnati.

Olofin ya ce Moniepoint zai yi amfani da fasaharsa da tsarin hada-hadar kuɗinsa domin tabbatar da cewa tsarin samun tallafin ya kasance mai sauƙi, inganci da tsaro.

Kara karanta wannan

Shin tallafin N50,000 da aka fara turawa 'yan Najeriya bashi ne ko kyauta? An samu bayani

Ya buƙaci kwastomomi su yi amfani da lambar USSD ta hukuma ta bankin kawai wajen tantance cancantarsu ko samun kuɗin tallafin.

Yadda mutum zai duba a Moniepoit

Ga matakan da masu amfani da Moniepoint za su bi domin tantance cancantarsu da karɓar tallafin N50,000 na Gwamnatin Tarayya:

  1. Danna lambar USSD: Buɗe wurin buga lambobi a wayarka, sannan ka danna *5573*27# ta amfani da lambar wayar da ka yi rajista da ita a asusun Moniepoint.
  2. Bi umarnin da aka bayar: Bi umarnin da zai bayyana a wayarka domin tantance cancantarka ga shirin NERSI.
  3. Amincewa da karɓar kuɗin: Idan an zaɓe ka, za ka ga saƙo a allon wayarka da zai buƙaci ka amince da karɓar tallafin N50,000.
  4. Karɓi kuɗin: Da zarar ka amince da tayin, za a tura kuɗin kai tsaye zuwa asusunka na Moniepoint.
Moniepoint.
Yadda aka bude manhajar Moniepoint a wayar hannu mai amfani da intanet Hoto: Moniepoit
Source: Facebook

Shin tallafin N50,000 bashi ne?

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta fara tura wa yan Najeriya masu karamin karfi tallafin N50000 duk wata karkashin shirin NERSI.

A sanarwar da ma'aikatar jin kai da yaki talauci ta fitar, gwamnatin ta bayyana cewa tallafin da aka fara turawa mutane ba bashi ba ne, kyauta ce domin rage wa talakawa radadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262