Ana ta mamaki da aka gano tsohon shugaba Jonathan yana da mata 2 bayan shekaru
- Ayima Lott-Jonathan za ta kaddamar da littafin da ta rubuta dangane da tarihin gwagwarmayar rayuwarta
- Marubuciyar littafin Gold Dust: Treasures of Quiet Years tana cikin matan Dr. Goodluck Ebele Jonathan na aure
- Duk da kasancewarsa kirista, bayan Dame Patience Jonathan, tsohon shugaban kasar yana da wata mata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja - Ayima Lott-Jonathan ta fito har duniya ta san ta, kuma wannan karo ta shirya rubuta littafin da yake dauke da tarihin rayuwarta.
Kusan a karon farko kenan da jama’a suke sanin Ayima Lott-Jonathan bayan ta yi kokarin janye jikinta a lokacin da mijinta yake mulki.
Jaridar The Cable ta ce Ayima Lott-Jonathan za ta kaddamar da littafinta da aka sanya wa suna ‘Gold Dust: Treasures of Quiet Years’
A ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamba 2026 za a kaddamar da wannan litafi a birnin tarayya Abuja.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo shi ne shugaban taron yayin da Bala Mohammed zai zama mai kaddamarwa.

Kara karanta wannan
Lamari ya yi tsanani har kotu tana yi wa ministan Tinubu barazana da dauri a kurkuku
Babban mai masaukin baki a ranar shi ne gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri tare da takwaransa na Rivers, Mai girma Siminalayi Fubara.
Uban taro a ranar zai zama Mai martaba Bubaraye Agada IV, zai jagoranci sauran sarakunan Bayelsa.
Babban bako na musamman shi ne mai gidanta, Goodluck Jonathan wanda ya kasance shugaban Najeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015.
Ita Lott-Jonathan ta karanci ilmin shari’a ne a jami’ar kimiyya da fasaha ta jihar Delta kuma tun a shekarar 2003 ta zama lauya a Najeriya.
Jaridar ta ce daga baya ta koma bangaren ilmi da tarbiyya da kuma harkokin shugabanci da gudanarwa har ta samu shaida daga NTI.
Baya ga haka ta yi digirin Masters da PhD daga jami’ar Walden University a kasar Amurka.
Ita ce ta kafa makarantar Aduvie International School da ke unguwar Jahi a Abuja bayan gidansu ya zama mataimakin shugaban Najeriya.
Littafin da ta rubuta yana kunshe da babi 12 dauke da tarihin rayuwarta musamman fadin-tashin da aka yi a yankin Neja Delta zuwa Abuja.
Ana sa rai littafin zai zama darasin rayuwa, hakuri, jajircewa da abin koyi da masu tasowa musamman matasa, mata da sauran iyaye.

Kara karanta wannan
Gwamna Radda ya yaye jami’an tsaron daji 1008 a Katsina, ya fadi aikin da za su yi
Alkaluma daga hukumomin Najeriya sun tabbatar da yadda auren mace fiye da guda ya shahara a wasu yankuna, ciki har da na Neja-Delta.
Jihar Bayelsa inda Goodluck Jonathan ya fito ita ce kan gaba domin akalla 10% na matan can suna zama da kishiya duk da yawanci kiristoci ne.
Dayar matarsa, Dame Patience ce ta zama uwargidar Najeriya da suke mulki tsakanin 2010 da 2015.
https://www.nigeriastats.com/FR395.pdf?utm_source=chatgpt.com
Asali: Legit.ng