Dubban Mutane Sun Samu Tallafin Abinci, Babura da Injunan Niƙa daga Tinubu

Dubban Mutane Sun Samu Tallafin Abinci, Babura da Injunan Niƙa daga Tinubu

  • Mutane da dama a jihar Zamfara sun amfana da tallafin kayan abinci, babura, injinan nika da kekunan ɗinki karkashin jagorancin Dr. Aslam Aliyu
  • Tsohon ɗan takarar majalisar dokokin jihar, Naziru Aliyu, ya yabawa Dr. Aslam kan yadda take kai tallafi ga al'umma
  • Naziru ya gode wa Shugaba Bola Tinubu tare da kira ga al'umma da su ci gaba da mara masa baya a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Mutane da dama a jihar Zamfara sun tallafi daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya domin ragewa al'umma raɗaɗin da suke ciki.

An raba kayan tallafin ne da suka hada da abinci, injunan nika, keken dinki da babura karkashin jagorancin yar gwagwarmaya, Dr. Aslam Aliyu.

An raba tallafin Tinubu a Zamfara
Dr. Aslam Aliyu da ta jagoranci raba tallafin Bola Tinubu a Zamfara. Hoto: Naziru Aliyu.
Source: Facebook

Wakilin Legit Hausa ya samu wannan bayani ne daga masoyin Tinubu kuma tsohon dan takarar majalisar jiha a Zamfara, Naziru Aliyu.

Kara karanta wannan

Abin da na jikin Tinubu suka gano wanda ya nuna Arewa na tare da shugaban ƙasa

Naziru ya bayyana rawar da Aslam ke takawa

Dan siyasar ya ce bayyana irin gudunmawar da Aslam Aliyu ke bayarwa wurin tabbatar da tallafin kaya ga al'umma.

Ya tura sakon godiya ga Bola Tinubu a madadin Aslam Aliyu inda ya ce tana shiga lunguna da sako domin jin koken al'umma.

A cewarsa:

"Dr. Aslam Aliyu mace ce wacce ta jajirce ta ke zagayawa kauyuka domin jin koken mutane da taimaka masu da tallafi.
"Mutane da dama ne suka samu tallafin karkashin Dr Aslam Aliyu da suka hada da babura, keken dinki, injin nika da kayan abinci da aka rabawa al'umma domin rage radadi kan wannan tsadar rayuwa da ake fama da ita."

Naziru Aliyu ya bayyana jin dadinsa inda ya ce wannan abin da yaba ne duba da halin da al'umma ke ciki.

Ya yaba wa Bola Tinubu da cewa suna kyautata tsammani zai kawo karshen radadin da ake fuskanta saboda mutum ne mai tausayi.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun afkawa masallata a sallar asuba a Zamfara, sun bindige hadimin gwamna

Dan siyasar ya bukaci al'umma da su ba shi goyon baya musamman a zaben da ke tafe domin a ceto kasa baki daya.

Matashi ya yaba wa Tinubu
Hon. Nazir Aliyu Kaura da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Naziru Aliyu, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.
Source: Facebook

Ya bukaci 'yan Najeriya su zabi Tinubu

Haka kuma, ɗan siyasar ya yi kira ga al'ummar Najeriya da su ci gaba da mara wa Shugaba Tinubu baya, musamman yayin da ake tunkarar zaɓe mai zuwa.

A cewarsa, ci gaba da goyon bayan shugaban zai taimaka wajen ƙoƙarin ceto ƙasar daga matsalolin da take fuskanta.

Hakan na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zaɓen shekarar 2027 a fadin Najeriya baki daya.

Naziru Kaura ya fadi alherin Tinubu a Arewa

Mun ba ku labarin cewa tsohon ɗan takarar majalisar dokokin Zamfara, Hon. Naziru Aliyu Kaura, ya bayyana nasarorin da Shugaba Bola Tinubu ya samu tun bayan hawansa mulki.

Ya ce gwamnatin Tinubu ta aiwatar da ayyukan tituna, tallafa wa ɗalibai da manoma tare da ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya.

Kaura ya buƙaci matasa su fito kwansu da kwarkwatarsu domin nuna goyon baya ga Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.