Cikin Sauƙi: Buratai Ya Faɗi Hanya 1 Ta Magance Ta'addanci har Abada

Cikin Sauƙi: Buratai Ya Faɗi Hanya 1 Ta Magance Ta'addanci har Abada

  • Tsohon babban hafsan sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai mai ritaya, ya ce ƙarfin soji kaɗai ba zai iya kawo ƙarshen ta'addanci a Najeriya ba
  • Buratai ya yi kira da a ƙara zuba jari a fannin ilimi domin bunƙasa tunanin matasa da magance matsalolin da ke haifar da ta'addanci
  • Tsohon hafsan sojin ya sanar da shirin bayar da cikakken tallafin karatu ga ƙwararrun ɗaliban da suka yi nasara a gasar rubuce-rubuce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – Tsohon babban hafsan sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai mai ritaya, ya bayyana cewa ilimi ne kaɗai zai iya kawo ƙarshen ta'addanci a Najeriya.

Buratai ya yi kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki da su ƙara zuba jari a fannin ilimi domin bunƙasa tunanin matasa, tare da magance matsalolin da ke haifar da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi.

Kara karanta wannan

Janar Buratai ya bayyana abu 1 da zai kawo karshen ta'addanci a Najeriya

Buratai ya magantu kan hanyar magance ta'addanci
Tsohon hafsan sojojin Najeriya, Tukur Buratai. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Twitter

Vanguard ta ce Buratai ya fadi hakan ne yayin bikin bayar da kyaututtukan gasar adabin matasa ta shekarar 2026 a Nasarawa.

Buratai ya bayyana muhimmancin ilimi

Tsohon hafsan sojin ya jaddada cewa bai kamata a dogara da ƙarfin makamai kaɗai wajen yaƙi da ta'addanci ba, yana mai cewa baiwar ilimi ce za ta iya magance matsalar tun daga tushenta.

Ya ce:

"Bindiga na iya kashe ɗan ta'adda, amma ilimi ne kaɗai zai iya kashe ta'addanci."

Buratai ya bayyana cewa ci gaban ƙasa bai tsaya ga samar da ababen more rayuwa, ƙarfin soji da tattalin arziki kawai ba, har da bunƙasa ilimi, basirar kirkire-kirkire da tarbiyyar al'umma.

Ya ce ya kamata matasan Najeriya, ba tare da la'akari da asalinsu ko matsayinsu ba, su samu dama da tallafin da za su bunƙasa baiwarsu tare da bayar da gudunmawa ga ci gaban ƙasa.

An kawo hanyar magance matsalar tsaro
Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Kiran da Buratai ya yi ga jami'o'i

Kara karanta wannan

Jita jita ta ƙare, an bayyana abin da aka tattauna tsakanin Peter Obi da 'yan Majalisar Amurka

Tsohon hafsan sojin ya ce an kafa gidauniyar ne bisa fahimtar cewa ƙasashe masu ci gaba ba wai ƙarfin soji da tattalin arziki ne kawai ke gina su ba, har da tunani, adabi da al'ummar da suka samu ingantaccen ilimi.

Ya buƙaci jami'o'i su ƙara ba da muhimmanci ga adabin matasa ta hanyar bincike, koyarwa da shirye-shiryen da ke ƙarfafa kirkire-kirkire, tunani mai zurfi da bunƙasa ilimi.

Buratai ya ce:

"Makarantar da ke samar da ɗalibai masu sakamako mai kyau amma ta yi watsi da kirkire-kirkire da tunani mai zurfi, ba ta shirya ɗalibanta yadda ya kamata domin fuskantar makomar rayuwa ba."

Ya bayyana cewa tun daga shekarar 2023, gidauniyar ta samar da dama ga matasan Najeriya daga sassa daban-daban domin nuna basirarsu ta rubuce-rubuce.

Ya ce ƙaddamar da kundin shekarar 2025 wani sabon ci gaba ne da zai adana ayyukan kirkire-kirkire da nasarorin matasa marubuta, cewar Punch.

Buratai ya musanta hannu a ta'addanci

A wani labarin, an ji cewa tsohon hafsan sojojin kasa a Najeriya, Tukur Yusuf Buratai ya magantu bayan saka sunansa cikin zargin taimakon ta'addanci.

Buratai ya yi karin haske ne kan zargin da ke cewa yana da hannun kai tsaye ko kaikaice wajen daukar nauyin ta’addanci.

Akwai mutane da dama ciki har da tsohon minista a gwamnatin Muhammadu Buhari da ake zarginsu da wannan mummunan laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.