'Yan Bindiga Sun Yi Sabon Ta'addanci cikin Dare a Plateau
- Ƙungiyar Mwaghavul Development Association ta ce wasu ’yan bindiga sun kashe aƙalla mutane tara a garin Zuwagal da ke masarautar Jipal
- Maharan sun kuma lalata gidaje da dama, kayan abinci da sauran dukiyoyi, musamman a ƙauyen Bong da ke ƙaramar hukumar Qua’an Pan
- Ƙungiyar ta ce al’ummar yankin sun samu bayanan sirri kan shirin kai hare-hare tun makonni biyu kafin aukuwar lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - Aƙalla mutane tara, ciki har da maza da mata, sun mutu bayan wasu ’yan bindiga sun kai sabon hari garin Zuwagal da ke masarautar Jipal, ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Plateau.
Shugabannin ƙungiyar Mwaghavul Development Association (MDA) sun ce harin ya faru ne a daren ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamban 2026 amma wahalar isa yankin da ƙarancin sadarwa sun kawo cikas wajen samun cikakkun bayanai.

Kara karanta wannan
"Ku kasance cikin shiri": Abin da Kwankwaso ya gayawa magoya baya bayan kai masa hari

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce lamarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan gwamnatin jihar ta ɗage dokar hana fita daga magariba zuwa wayewar gari da ta sanya a Mangu da wasu ƙananan hukumomi biyu sakamakon hare-hare da kashe-kashe.
Gwamnatin jihar ta sanar a ranar Alhamis cewa ta ɗage dokar ne bayan tattaunawa da jami’an tsaro.
Yadda ’yan bindigar suka kai harin
Shugaban kungiyar MDA na kasa, Bulus Dabit, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce an tura jami’an tsaro zuwa yankin.
Dabit ya bayyana cewa maharan sun shiga garin ne a lokacin da mazauna yankin suke barci, inda ya bayyana harin a matsayin wanda aka kai ba tare da wani dalili ba.
A cewarsa:
"A daren jiya, ’yan bindiga sun kai hari Zuwagal, wani gari da ke da wahalar isa a masarautar Jipal, da kuma ƙauyen Bong da ke maƙwabtaka da shi a ƙaramar hukumar Qua’an Pan.
“Harin ya yi sanadin mutuwar mutane tara a Zuwagal, tare da lalata gidaje da dama, kayan abinci da sauran dukiyoyi, musamman a Bong.”
An yi jana’izar mamatan
Shugaban MDA ya ce an kwashe gawarwakin waɗanda aka kashe da safiyar ranar Talata, 17 ga watan Nuwamban 2026 sannan aka yi musu jana’izar bai ɗaya a Zuwagal.
Ya ce an gudanar da jana’izar ne a gaban jami’an tsaro, hukumomin ƙananan hukumomin Mangu da Qua’an Pan, wakilan sarakunan gargajiya da kuma shugabannin ƙungiyar MDA.
An samu bayanan sirri kafin harin
Al’ummar yankin sun yi zargin cewa sun shafe makonni biyu suna samun bayanan sirri game da shirin kai musu hari, kuma sun ce sun miƙa bayanan ga jami’an tsaro.
Sai dai MDA ta buƙaci jami’an tsaro su ci gaba da gudanar da ayyukansu domin rusa hanyoyin sadarwar ’yan ta’adda a ƙaramar hukumar Qua’an Pan ta Plateau da kuma ƙaramar hukumar Awe ta Jihar Nasarawa.
A cewar ƙungiyar, waɗannan yankuna suna da iyaka da ƙaramar hukumar Mangu, lamarin da ya sa take ganin akwai buƙatar ƙarfafa sintiri da ayyukan tsaro.
Dabit ya ce ba za a samu adalci ga waɗanda aka kashe ba har sai an gano waɗanda suka aikata laifin, an kama su kuma an gurfanar da su a gaban kotu.
A halin da ake ciki, Kyaftin Polycap Oteh, mai magana da yawun rundunar Operation Enduring Peace, wadda jami’anta suke aiki a yankin, bai mayar da martani ga tambayoyin wakilinmu ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Source: Original
'Yan bindiga sun sace yara a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ’yan bindiga sun kashe wani jami’in tsaro tare da sace wasu ’yan gidan wani ɗan kasuwa, Alhaji Babangida Sama’ila, a Sabuwar Kaura, ƙaramar hukumar Kaura Namoda ta Jihar Zamfara.
Maharan sun kai farmakin ne a gidan ɗan kasuwar, inda suka yi awon gaba da wasu ’yan mata uku, mahaifiyarsu da yara maza biyu, tare da wani baƙo da ya ziyarci iyalin.
Asali: Legit.ng

