Obi da Kwankwaso Sun Tallata Surukin Buhari da ke Takarar Sanata a Jam’iyyar NDC

Obi da Kwankwaso Sun Tallata Surukin Buhari da ke Takarar Sanata a Jam’iyyar NDC

  • Muhammad Turad Sha’aban ya fito takarar Majalisar dattawa, ya tsaya a karkashin jam’iyyar adawa ta NDC
  • Rabiu Kwankwaso da Peter Obi sun hadu da matashin ‘dan siyasar kuma sun kaddamar da ofishin yakin neman zabensa
  • Turad Sha’aban yana sa rai ya doke Sanata mai-ci, Khalid Ibrahim Soba na ADC da Mukhtar Ramalan a APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kaduna - Muhammad Turad Sha’aban yana neman zama sanata a Majalisar dattawa a 2027 a karkashin jam’iyyar adawa ta NDC.

Muhammad Turad Sha’aban ya shiga harkar siyasa gadan-gadan, wannan karo ya ci burin wakiltar mutanen Arewacin Kaduna a majalisa.

Turad Sha'aban
Turad Sha'aban tare da Rabiu Kwankwaso da Peter Obi a taron jam’iyyar NDC a Zariya Hoto: @SaifullahiHon
Source: Twitter

Turad Sha'aban yana neman zama sanata

Dr. Abubakar Hidima a shafinsa na X kwanaki, ya wallafa bidiyon matashin inda aka ji yana rokon jama’a su ba shi kuri’arsu ya wakilce su.

Turad Sha’aban ya koka game da yadda sanatoci suka zama ‘yan amshin shatan shugaban kasa, ya ce idan aka zabe shi, ba zai biye masu ba.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun tarwatsa gangamin APC a Borno, sojoji sun kai dauki

Matashin yake cewa sakamakon kyale shugaban kasa da Majalisar tarayya ta yi, ana fama da matsin rayuwa, tsadar abinci da kuma tulin haraji.

Nasaba da tarihin Turad Sha'aban

Yanzu haka shi ne Wakilin Tudun Wadan Zazzau kuma ya fito daga babban gida a Zariya, mahaifinsa shi ne Hon. Sani Muhammad Sha’aban.

Shi ma Sani Sha’aban wato Dan Buram Zazzau ya taba zama ‘dan majalisar tarayya lokacin ANPP.

Turad Sha’aban ya yi karatun firamare a Zaria Children da Zariya Academy daga 1992 zuwa 2004, daga nan ya tafi birnin Dubai domin samun digiri.

Bayan digirinsa a harkar ilmin kudi da tattali, sai ya tafi jami’ar University of Northampton a Birtaniya domin samun digirgir a fannin kasuwanci (MBA).

A ina Turad ya yi aiki a baya?

An ce ya yi aiki da kamfanoni irinsu Nexus Financial Advice, DAMAC Properties, Nigeria LNG da kuma hukumar NDIA kafin shiga gwamnati.

Surukin na marigayi Muhammadu Buhari ya yi aiki da Babatunde Raji Fashola lokacin yana kujerar babban Ministan gidaje da ayyuka a baya.

Kara karanta wannan

An zabi sabon shugaban majalisar Isra'ila, Netanyahu ya rasa karfin iko

‘Dan takaran ya kware a sha’anin kudi, kasuwanci, tattalin arziki, gine-gine da kuma aikin gwamnati.

Turad Sha'aban
Turad Sha'aban lokacin aurensa da Hanan Muhammadu Buhari a Abuja Hoto: @aishambuhari
Source: Instagram

Jam'iyyar NDC sun bude masa ofishin kamfe

Da Rabiu Kwankwaso da Peter Obi suka zo Zariya a ranar 14 ga watan Nuwamba 2026, sun tallata takarar Muhammad Turad Shuaibu da kyau.

‘Yan takaran sun yi zama da ‘yan jam’iyyar NDC, mabiya Kwankwasiyya da ‘yan tafiyar Obidient kamar yadda hadimin Kwankwaso ya wallafa a X.

Bayan taron da aka yi a Kongo Conference Hotel, Kwankwaso a shafinsa ya sanar da cewa ya kaddamar da ofishin yakin zaben Turad Sha’aban.

An kai wa 'yan NDC hari a Kano

An ji labari tawagar Rabiu Musa Kwankwaso da Aminu Abdussalam Gwarzo ta ci karo da ‘yan daba har an yi wa NDC barna wajen kamfe a Kano.

A cikin karamar hukumar Bichi a Kano, wasu da ake zargi da ’yan daba ne sun kai hari kan ayarin motocin tsohon gwamnan a yayin kamfen.

An jefa su da duwatsu, wasu ’yan tawagar sun ji rauni, kuma an farfasa motoci kusan bakwai. Sai dai gwamnatin Kano ta ce labarin ba gaskiya ba ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng