Jiragen Kasa za Su Fara Yawo a Arewa, Tinubu zai Bude Tashar Jirgi a Kano

Jiragen Kasa za Su Fara Yawo a Arewa, Tinubu zai Bude Tashar Jirgi a Kano

  • Gwamnatin tarayya ta ce aikin layin dogo na Kaduna zuwa Kano ya kai kashi 90 cikin 100, kuma za a ƙaddamar da shi ranar 3 ga Disamba, 2026
  • Haka kuma, aikin layin dogo na Kano zuwa Katsina da Maradi ya kai kashi 70 cikin 100, a cewar majalisar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta APC
  • Shugaba Bola Tinubu ya kuma bayar da umarnin kammala batutuwan filaye da biyan diyya da suka rage a cikin birnin Kaduna domin kammala aikin

Kara karanta wannan

"Ko a jiki na," Atiku ya maida martani bayan kotu ta rushe takararsa a zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna – Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta jam’iyyar APC ta sanar da cewa Shugaba Bola Tinubu zai ƙaddamar da aikin layin dogo na zamani daga Kaduna zuwa Kano ranar 3 ga Disamba, 2026.

Kakakin kwamitin kuma Ministan Ma’adinai, Dele Alake, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, inda ya ce aikin layin dogo mai tsawon kilomita 203 daga Kaduna zuwa Zariya da Kano ya kai kashi 90 cikin 100.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya fito yana murna da rusa takarar Atiku da dukkan 'yan ADC a Najeriya

Jiragen kasa a Arewacin Najeriya
Yadda tashohin jiragen kasa ke kokarin fara aiki. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Alake ya kuma bayyana cewa aikin layin dogo mai tsawon kilomita 400 daga Kano zuwa Katsina da Maradi a Jamhuriyar Nijar ya kai kashi 70 cikin 100.

Aikin layukan dogon na cigaba

A cewar sanarwar da Bayo Onanuga ya wallafa a X, lokacin da Tinubu ya hau mulki a shekarar 2023, aikin layin dogo na Kaduna zuwa Kano bai kai kashi 30 cikin 100 na kammalawa ba.

Haka kuma, aikin Kano zuwa Katsina da Maradi yana a matakin kashi biyar cikin 100 kacal a lokacin.

Kwamitin yaƙin neman zaɓen ta ce ci gaban da aka samu ya nuna ƙudurin gwamnatin Tinubu na faɗaɗa hanyoyin sufuri na jiragen ƙasa, inganta zirga-zirga da sauƙaƙa jigilar fasinjoji da kayayyaki a Najeriya da ƙasashen da ke makwabtaka da ita.

Kara karanta wannan

Matasa sun hargitsa wajen da Shettima ya je kamfe din APC na 2027

Karin bayani daga gwamnati

Sanarwar ta bayyana cewa wata tawagar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Babban Sakataren Ma’aikatar Sufuri, Funso Adebiyi, ta duba ayyukan biyu bisa umarnin Shugaba Tinubu.

Tawagar ta bayyana gamsuwarta da ingancin aikin, musamman yadda aka shimfiɗa layin dogon, magudanan ruwa, kariyar tudu da kuma matakan ƙarfafa ƙasa.

Haka kuma, tawagar ta yi gwajin tafiyar jirgin ƙasa daga Jaji a jihar Kaduna zuwa Kano domin duba yanayin layin dogon da jin daɗin fasinjoji.

Za a kammala biyan diyya

Kwamitin yaƙin neman zaɓen ya ce Tinubu ya bayar da umarnin warware dukkan matsalolin mallakar filaye da biyan diyya da suka rage a cikin birnin Kaduna cikin gaggawa domin kammala hanyar jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kano.

Kara karanta wannan

Indonesia: An yi wa shugaban kasa kutse a waya, an saurari maganganun da yake yi

Ya bayyana cewa za a ƙaddamar da ɓangaren Jaji zuwa Kano mai tsawon kilomita 190 daga cikin jimillar kilomita 205 na aikin Kaduna zuwa Kano.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na yi wa jama'a bayani. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Haka kuma, za a ƙaddamar da ɓangaren Dawanu zuwa Kano, Kazaure, Daura da Katsina mai tsawon kilomita 250 na aikin Kano zuwa Maradi a ranar 3 ga Disamba, 2026.

A cewar kwamitin yaƙin neman zaɓen APC, layin dogon Kaduna zuwa Kano zai haɗu da layin dogon zamani na Abuja zuwa Kaduna, wanda hakan zai samar da hanyar jirgin ƙasa kai tsaye tsakanin Abuja, Kaduna, Zariya da Kano.

Tinubu ya kaddamar da tallafi

A wani labarin, mun ruwaito cewa SMEDAN ta ƙaddamar da wani shiri da ke da burin samar da hamshakan ’yan kasuwa 100 ta hanyar horo da tallafin kuɗi.

Rahoto ya nuna cewa shirin zai ƙunshi gasar gabatar da dabarun kasuwanci tare da kyautar Naira miliyan 100 domin tallafa wa ƙananan ’yan kasuwa.

An bayyana cewa za a raba tallafin ne a taron GROW Nigerian na shekarar 2026 da kuma wani taro da za a gudanar a Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng