Gwamnatin Tarayya Ta Faɗi Yankuna da Jihohin da Su Ci Moriyar Tallafin N50,000
- Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa shirin tallafin Naira 50,000 na NERSI ya shafi jihohi 36 da Abuja, a dukkan shiyyoyin Najeriya
- Ma’aikatar jin ƙai ta bayyana cewa ba sai an cike fom ko yin rajista ba kafin a zaɓi waɗanda za su amfana da tallafin
- Za a aika wa waɗanda aka zaɓa saƙon SMS daga hukumomin kuɗi da aka amince da su domin sanar da su lokacin karɓar tallafin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Gwamnatin tarayya ta yi ƙarin haske kan ci gaba da raba tallafin N50,000 da aka yi ga yan Najeriya saboda rage masu radadi.
Gwamnatin ta bayyana cewa shirin tallafin Naira 50,000 na NERSI ya shafi gidaje masu ƙaramin ƙarfi a dukkan shiyyoyin siyasa shida na Najeriya, ciki har da jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja.

Source: Twitter
Rahoton NTA News ya ce Ma’aikatar Jin Ƙai da Rage Talauci ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da daraktar yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Janet Mcdickson Noah, ta fitar ranar Juma’a, 6 ga watan Nuwambar 2026.
Sanarwar ta biyo bayan tambayoyin da al'umma ke yi game da jihohin da shirin tallafin ya shafa da kuma waɗanda suka cancanci amfana.
Jihohin da shirin NERSI ya shafa
Ma’aikatar ta bayyana cewa shirin ya shafi jihohi shida na Kudu maso Yamma, waɗanda suka haɗa da Legas, Oyo, Ogun, Osun, Ondo da Ekiti.
A Kudu maso Gabas kuwa, jihohin da shirin ya shafa su ne Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu da Imo.
Haka kuma, jihohin Kudu maso Kudu sun haɗa da Akwa Ibom, Bayelsa, Cross River, Delta, Edo da Rivers.
A Arewa ta Tsakiya kuwa, jihohin sun haɗa da Benue, Kogi, Kwara, Nasarawa, Neja da Filato, tare da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Jihohin Arewa maso Gabas da za su amfana su ne Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe, cewar Punch.
A Arewa maso Yamma kuwa, jihohin sun haɗa da Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara.

Source: Getty Images
Yadda gwamnati ke zaɓar waɗanda za su amfana
Ma’aikatar ta bayyana cewa ana zaɓar waɗanda za su amfana ne daga rajistar masu ƙaramin ƙarfi ta ƙasa (National Social Register), tare da tantance bayanan shaidar ɗan kasa.
Ta ce ana yin zaɓen ne bisa la'akari da yanayin talauci da kuma raunin tattalin arzikin iyalan da ake son tallafawa.
Sai dai ma’aikatar ta jaddada cewa babu wata jiha da aka fitar da cikakken jerin sunayen mutanen da za su amfana da tallafin N50,000.
Ta kuma yi gargaɗin cewa babu buƙatar cike fom ko shiga wata manhaja domin neman tallafin.
Haka zalika, ta bayyana cewa babu wani mutum, jami’in gwamnati ko wakili da ke da ikon yin katsalandan wajen zaɓen waɗanda za su amfana.
Ma’aikatar ta ƙara da cewa tallafin Naira 50,000 kyauta ne, don haka babu buƙatar wanda ya karɓa ya mayar da kuɗin.
Tallafin N50, 000: Shafukan da mutum zai shiga
An ji cewa Gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan shirin tallafin N50,000 yayin da aka fara yada wasu shafukan yanar gizo na damfara.
Ma’aikatar jin kai ta ce tallafin N50,000 na musamman ne ga talakawa da gidajen da ke cikin mawuyacin hali sakamakon tsadar rayuwa.
Ta ce ba a bukatar mutane su cike fom ko yin rajista, domin za a zabi wadanda suka cancanta daga rajistar marasa galihu ta kasa.
Asali: Legit.ng


