Nafiu Bala Ya Sake Taso Atiku a Gaba duk da Nasara a Kotu
- Shugaban wani ɓangare na ADC, Nafiu Bala, ya zargi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da yin watsi da doka ta hanyar ci gaba da kamfen
- Nafiu Bala ya ce ƙin bin kundin tsarin mulkin ADC na jefa shakku kan ko Atiku zai mutunta kundin tsarin mulkin Najeriya idan ya zama shugaban ƙasa
- Ya bayyana cewa ci gaba da kamfen duk da hukuncin kotu da ya shafi ɓangaren Atiku tamkar hauka ne da rashin kulawa da doka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Nafiu Bala, shugaban wani ɓangare na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), ya yi zargi kan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
Nafiu Bala ya zargi Atiku Abubakar da yin watsi da bin doka ta hanyar ci gaba da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa duk da hukuncin kotu kan rikicin shugabancin jam'iyyar.

Source: Facebook
Nafiu Bala ya yi wannan zargi ne ranar Lahadi, 8 ga watan Nuwamban 2026 yayin da yake mayar da martani ga jaridar Leadership.
Ya ce zargin cewa Atiku ya ƙi bin kundin tsarin mulkin ADC ya haifar da tambayoyi kan ko zai mutunta kundin tsarin mulkin Najeriya idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa. A cewarsa, duk mutumin da ba ya son bin doka bai cancanci jagorantar ƙasar ba.
Nafiu Bala ya soki ci gaba da kamfen ɗin Atiku
Shugaban ɓangaren ADC ɗin ya ƙara da cewa idan kotu ta bayyana ɓangaren Atiku da matakan da ya ɗauka a matsayin waɗanda ba su da inganci, ci gaba da harkokin yaƙin neman zaɓe duk da hukuncin tamkar rashin hankali ne.
Ya bayyana cewa irin wannan mataki na nuna rashin kulawa da dokokin ƙasa da na jam'iyya.
Nafiu Bala ya ce:
“Wannan ya tabbatar karara cewa Atiku Abubakar bai taɓa ɗaukar doka da muhimmanci ba. Wannan ne ya sa tun farko ya ƙi bin kundin tsarin mulkin jam'iyyar ADC.

Kara karanta wannan
Amaechi ya hango abin da zai haddasa yakin basasa a Najeriya ana batun zaben 2027
“Idan mutum ya ƙi bin kundin tsarin mulkin ADC, ta yaya za mu sa ran zai bi kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya? Duk wanda ya ƙi bin doka bai cancanci zama shugaban Najeriya ba.”
Ya yi magana kan hukuncin kotu
Nafiu Bala ya kuma yi zargin cewa idan kotu ta bayar da umarnin soke ɓangaren Atiku tare da bayyana cewa duk matakan da suka ɗauka ba su da inganci kuma ba su da tushe a doka, bai kamata ya ci gaba da kamfen ba.
Ya ce ci gaba da gudanar da harkokin siyasa duk da irin wannan hukunci abin da ya kira hauka ne da rashin kulawa da doka.
A kalamansa:
"Idan kotu ta bayar da umarnin cewa ɓangaren da ya ƙirƙira ba shi da inganci, sannan ta yanke cewa duk abin da suka yi ba shi da inganci kuma ba shi da tushe a doka, amma duk da haka ya ci gaba da kamfen, za mu ɗauki hakan a matsayin hauka da kuma rashin kulawa da doka.”
Zargin na Bala na zuwa ne yayin da rikicin shugabancin ADC ke ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce, musamman kan halaccin shugabancin jam'iyyar da matakan da ɓangarorin da ke rikici suka ɗauka.

Source: Twitter
ADC ta samu goyon baya
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar jam’iyyun adawa ta Coalition for Democracy, mai ƙunshe da jam’iyyu tara, ta bayyana goyon bayanta ga jam’iyyar ADC bayan kotun tarayya ta soke shugabancin jam’iyyar ƙarƙashin Sanata David Mark.
Ƙungiyar ta bayyana hukuncin kotun da aka yanke a matsayin wani mataki mai haɗari da ka iya zama wani shiri na kawar da sahihan jam’iyyun adawa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Asali: Legit.ng

