Arewa Ta Barke da Murna Bayan Ware $1.3Bn Kan Aikin Layin Dogo Daga Kano Zuwa Maradi

Arewa Ta Barke da Murna Bayan Ware $1.3Bn Kan Aikin Layin Dogo Daga Kano Zuwa Maradi

  • A kokarin Gwamnatin Tarayya wurin inganta sufuri, ta yi nasarar samun $1.3bn domin karasa aikin layin dogo daga Kano zuwa Maradi
  • Ministan sufuri a Najeriya, Sanata Sa’idu Alkali ya bayyana haka ga ‘yan jaridu inda ya ce hanyar za ta bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu
  • Tun a mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne aka kaddamar da gina haryar jirgin kasa ta Kano-Katsina-Jibiya zuwa Maradi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Ma’aikatar sufuri a Najeriya ta ware $1.3bn domin kammala hanyar jirgin kasa ta Kano zuwa Katsina har birnin Maradi.

Ministan sufuri, Sa’idu Alkali ya bayyana haka a Facebook a jiya Talata 12 ga watan Maris a Abuja inda ya ce wannan babbar nasara ce.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya amince zai raba tallafin abinci ga talakawa sama da miliyan 2 a Ramadan

Za a ci gaba da aikin jirgin kasa na Kano zuwa Katsina har zuwa Maradi
Gwamnatin ta tabbatar da cewa aikin zai inganta alakar kasuwanci tsakanin Najeriya da Nijar. Hoto: Bola Tinubu, @MinTransfortationNG.
Asali: Facebook

Yawan kason da gwamnati za ta biya

Alkali ya ce kamfanin kasar Sin na CCECC zai ba da kaso 85 na kudin aikin jirgin kasa yayin da gwamnati za ta biya kaso 15, cewar Thisday.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na daga cikin himmatuwar Gwamnatin Tarayya wurin inganta harkokin kasuwanci musamman tsakanin Najeriya da Nijar.

Hadimin ministan a bangaren hulda da jama’a, Jamilu Ja’afaru ya ce wannan aiki zai kara inganta alaka tsakanin kasashen biyu da suke da al’adu iri daya.

Muhimmancin karasa aikin layin dogon

“Hanyar jirgin kasa ta Kano zuwa Katsian har Maradi zai inganta tattalin arzikin kasashen Najeriya da Nijar.”
“Yayin da ake ci gaba da aikin, gwamnatin Najeriya ta himmatu wurin tabbatar da samun ci gaba da kuma zaman lafiya.”
“Ministan Sufuri zai ci gaba da ba da rahoton yanayin aikin da kuma kokarin inganta bangaren sufuri da ya ke yi.”

Kara karanta wannan

Mutane miliyan 1.25 za su ci gajiyar shirin tallafin Ramadan daga hannun Sanata Yari

- Jamilu Ja’afaru

Buhari ne ya kaddamar da aikin

Kun ji cewa gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta kaddamar da gina layin dogo daga Kano zuwa kasar Nijar.

Layin dogon da gwamnatin ta rattaba hannu a kai zai bi Kano zuwa Katsina har zuwa birnin Maradi na Jamhuriyar Nijar.

Masana sun tabbatar da cewa gina wannan layin dogo zai yi matukar tasiri wurin inganta alakar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel