Amaechi Ya Hango Abin da Zai Haddasa Yakin Basasa a Najeriya Ana Batun Zaben 2027

Amaechi Ya Hango Abin da Zai Haddasa Yakin Basasa a Najeriya Ana Batun Zaben 2027

  • Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na ADC, Rotimi Amaechi, ya ce hukuncin kotu kan shugabancin jam'iyyar na iya jawo rikici
  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke shugabancin David Mark, tare da rushe tsarin da ya samar da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027
  • Amaechi ya musanta cewa akwai rikicin cikin gida a ADC, yana mai zargin cewa tsoron APC ne ya haddasa ƙalubalantar shugabancin jam'iyyar a kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Rotimi Amaechi, ya yi gargaɗin cewa hukuncin kotu kan shugabancin jam'iyyar na iya haddasa rikici idan ba a tafiyar da lamarin cikin hikima ba.

Amaechi ya bayyana cewa hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke kan shugabancin jam'iyyar na iya haifar da mummunan sakamako ga ƙasar idan aka kasa shawo kan lamarin.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Matakin da INEC za ta dauka kan rusa takarar Atiku a 2027

Amaechi ya yi gargadi kan zaben 2027
Rotimi Amaechi tare da Alhaji Atiku Abubakar Hoto: @atiku
Source: Twitter

Amaechi ya yi gargaɗin yiwuwar rikici

Da yake magana a wata hira da gidan rediyon Mainland 98.3FM, Amaechi ya ce hukuncin na iya haddasa yaƙin basasa idan ba a kula da shi yadda ya kamata ba.

Ya ce bayan samun labarin hukuncin, shi da Atiku da shugaban jam'iyyar sun gudanar da taro cikin gaggawa domin neman hanyar da za a bi wajen kwantar da hankula.

A kalamansa:

“Zai iya haddasa yaƙin basasa idan ba a kula da lamarin yadda ya kamata ba. Da muka ji labarin, ni da ɗan takarar shugaban ƙasa da shugaban jam'iyyar muka yi gaggawar zama, sannan muka ce: ‘Don Allah, a rage zafin lamarin’.”

Amaechi ya ce akwai takardar da Nafiu Gombe ya sanya wa hannu, wadda ta nuna cewa ya yi murabus a lokaci guda da tsohon shugaban jam'iyyar, Ralph Nwosu.

Ya kuma yi iƙirarin cewa akwai bidiyon da ke nuna Gombe a bayan David Mark lokacin da ake miƙa masa ragamar shugabancin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Zance ya kare: Atiku ya bayyana makomar takararsa a 2027 bayan hukuncin kotu

Ya zargi wasu da amfani da kuɗi wajen shigar da ƙara

Amaechi ya zargi wasu mutane da ɗaukar matakan shigar da ƙara a kotu ta hanyar biyan kuɗi da kuma yin abin da ya kira katsalandan a wasu sassan tsarin.

"Suna zuwa su ɗauki lauyoyi, su biya kuɗi, su je kotu, sannan su lalata wasu sassa na tsarin nan da can.” In ji shi.

Sai dai Amaechi ya musanta cewa akwai rikicin cikin gida a ADC, yana mai cewa ƙalubalen da jam'iyyar ke fuskanta ya samo asali ne daga tsoron da APC ke yi mata.

“Babu wani rikicin cikin gida a jam'iyyarmu, ko kaɗan. Abin da ake gani kawai shi ne tsoron All Progressives Congress (APC).” In ji shi

Kotun ta soke shugabancin David Mark

Mai Shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin da ya soke shugabancin kwamitin riƙon ƙwarya na David Mark.

Kotun ta kuma soke zaɓen Rauf Aregbesola, tsohon ministan harkokin cikin gida, a matsayin sakataren jam'iyyar na ƙasa, da sauran matakan da shugabancin Mark ya ɗauka.

Kara karanta wannan

Zaɓi 2 da suka rage wa Atiku bayan rushe takararsa, shugabannin ADC

Haka kuma, hukuncin ya shafi zabar ’yan takara domin neman muƙaman zaɓe a ƙarƙashin jam'iyyar.

Kotun ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da kada ta amince da matakan da aka ɗauka a taron kwamitin zartarwa na ƙasa karo na 99 na ADC, wanda aka gudanar ranar 27 ga Yuli, 2025.

Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da tsohon mataimakin shugaban ADC na ƙasa mai kula da shiyyar Arewa maso Gabas, Nafiu Gombe, ya shigar.

Nafiu Gombe ya ƙalubalanci tsarin da David Mark da sauran mambobin kwamitin riƙon ƙwarya suka bi wajen karɓar shugabancin jam'iyyar.

Amaechi ya yi magana kan hukuncin kotu
Rotimi Amaechi tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Twitter

Amaechi ya yi magana kan Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa Rotimi Amaechi, ya dora alhakin kayen da ya sha a zaben fitar da gwani na APC na 2022 kan Shugaba Muhammadu Buhari.

Amaechi ya ce ya fadi zaben ne sakamakon shawarar da ya ce ya bi ta marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na kada ya yi wahalar neman goyon baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng