Ba a gama surutu ba, Tinubu yana harin karbo danyen bashin $500m daga bankin duniya

Ba a gama surutu ba, Tinubu yana harin karbo danyen bashin $500m daga bankin duniya

  • Gwamnatin Tarayya na neman kudi daga Bankin Duniya domin kafa tsarin samar da ayyukan more rayuwa a Najeriya
  • Ana sa ran amincewa da bashin a ranar 25 ga Mayun 2027, kwanaki kafin rantsar da wanda zai hau kujerar shugaban kasa
  • Shirin na cikin wani babban tsarin zuba jarin dala biliyan 3.85 da nufin gina abubuwan more rayuwa da samar da ayyuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya na neman sabon bashin dala miliyan 500 daga Bankin Duniya domin a gudanar da manyan ayyukan more rayuwa.

Punch ta rahoto cewa ana sa ran Bankin Duniya zai amince da bashin a ranar 25 ga Mayun 2027, wato kwanaki hudu kafin rantsar da shugaban kasa Najeriya.

Shugaba Bola Tinubu ko wanda ya doke shi a zabe zai shiga ofis a ranar 29 ga Mayun 2027.

Wannan sabon yunkurin neman bashi na zuwa ne a daidai lokacin da harkokin siyasa ke kara zafi gabanin babban zaben 2027, lamarin da ya jawo tambayoyi.

Kara karanta wannan

Sama da kasa ba za su hade ba idan aka hana Atiku takara in ji ministan Tinubu

A cewar wata takarda da Bankin Duniya ya fitar, bashin na cikin wani babban shirin samar da kudin samar da ayyukan more rayuwa da ya kai dala biliyan 3.85.

Shirin mai suna Nigeria Infrastructure Financing and De-Risking Platform for Growth and Jobs, wanda aka fi sani da INFRAGROW zai bunkasa tattalin arziki.

Manufar ita ce jawo hankalin masu zuba jari daga kamfanoni masu zaman kansu domin bunkasa muhimman sassan tattalin arzikin Najeriya kuma a samu ayyuka.

Ma'aikatar Kudi ta Tarayya ce za ta karbi bashin, yayin da Hukumar Kula da Zuba Jarin Najeriya (NSIA) za ta kula da aiwatar da shirin kamar yadda aka ruwaito.

Bankin Duniya ya tsara zai duba takardun a ranar 21 ga Janairun 2027, ranar 25 ga Mayun 2027 aka ware domin amincewa da bashin da Najeriya ta ke son karba.

Wannan na nufin akwai yiwuwar a amince da bashin a kwanakin karshe na wa'adin mulkin Shugaba Bola Tinubu wanda yake sa ran ya zarce har zuwa 2031.

Sai dai amincewa da bashin ba yana nufin za a fitar da kudin ko fara aiwatar da shirin nan take ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi yadda ya yi tukin tasi domin rufa wa kansa asiri a Amurka

Har yanzu dai Bankin Duniya bai amince da bukatar bashin ba, kuma jadawalin da aka fitar na iya sauyawa don haka kudin ba za su shigo hannun Najeriya a lokacin ba.

Hikimar neman bashi daga Bankin duniya

Takardar babban bankin na duniya ta bayyana cewa Najeriya na fama da gibin kudin samar da ayyukan more rayuwa da ya kai kusan dala biliyan 100 a duk shekara.

Bankin ya ce karancin zuba jari da kuma rashin kyakkyawan shiri kafin fara manyan ayyuka na daga cikin matsalolin da ke kawo cikas ga bunkasar tattalin arzikin kasar.

Ya nuna matsalar ba ta tsaya ga rashin kudi kadai ba, har da wahalar mayar da kudin da ake da su zuwa ayyukan more rayuwa da za su iya jawo hankalin masu zuba jari.

Dala miliyan 500 da ake nema daga bankin za ta kunshi dala miliyan 400 daga Bankin Raya Kasa da Kasa (IBRD) da kuma dala miliyan 100 daga IDA ta raya kasashe.

Yadda za a samar da sauran kudaden

Baya ga bashin, shirin na $3bn zai kunshi gudummawar gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu, bankunan kasuwanci da wasu hukumomin hada-hadar kudi na duniya.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya yi gargaɗi ga Tinubu, ya faɗi bala'in da ke tunkarar Najeriya

Hukumar NSIA za ta zuba dala miliyan 200 a matsayin jarin farko, yayin da masu zuba jari daga kamfanoni masu zaman kansu su ma za su bayar da dala miliyan 200.

Haka kuma, ana sa ran samun dala miliyan 600 daga bashin da za a karbo hannun bankunan kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng