Babbar Nadamar da Kwankwaso Ya Yi a Zaɓen 2023 da Tinubu Ya Yi Nasara

Babbar Nadamar da Kwankwaso Ya Yi a Zaɓen 2023 da Tinubu Ya Yi Nasara

  • Rabiu Kwankwaso ya bayyana nadamarsa kan ƙin amincewa da haɗa tikiti da Peter Obi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023
  • Tsohon gwamnan Kano ya ce da ya fahimci Obi sosai a wancan lokaci, da sun haɗa kai sun kayar da APC
  • Kwankwaso ya bayyana cewa Obi ya amince zai jagoranci ma’aikatar ilimi idan jam’iyyar NDC ta lashe zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana nadamarsa kan ƙin amincewa da haɗa kai da Peter Obi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Rabiu Kwankwaso, wanda yanzu yake takarar mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar NDC ya ce da ya fahimci Obi sosai a wancan lokaci, da sun yi haɗin gwiwa sun kayar da jam’iyyar APC.

Kwankwaso ya tuna zaben 2023
Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi, Sanata Seriake Dickson da Rabiu Kwankwaso. Hoto: Mr Peter Obi.
Source: Facebook

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Kwankwaso ya bayyana hakan ne ranar Asabar a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar a cibiyar taro ta 360.

Kwankwaso ya yi nadamar ƙin haɗa kai da Obi

Da yake jawabi a wajen taron, Kwankwaso ya ce bai fahimci halin Peter Obi sosai ba a lokacin zaɓen 2023, amma yanzu ya fahimci irin gudunmawar da haɗin kansu zai iya bayarwa.

A kalamansa:

“Ban fahimci Peter Obi sosai ba sai yanzu. Da a ce na fahimce shi sosai a shekarar 2023, da mun haɗa kai mun kawar da jam’iyyar All Progressives Congress daga mulkin shugaban ƙasa.”

A zaɓen 2023, Kwankwaso ya tsaya takara ne a ƙarƙashin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), yayin da Obi ya tsaya takara a jam’iyyar Labour.

Kwankwaso ya samu ƙuri’u 1,496,687, inda ya zo na huɗu, tare da lashe jihar Kano kaɗai. Shi kuwa Obi ya samu ƙuri’u 6,101,533, inda ya zo na uku bayan ya lashe jihohi 12 da Abuja.

A jimlace, ƙuri'un 'yan takarar biyu sun kai 7,598,220, yayin da Bola Tinubu na APC ya lashe zaɓen da ƙuri'u 8,794,726.

Kwankwaso zai jagoranci bangaren ilimi
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso daga jihar Kano. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Twitter

Kwankwaso zai jagoranci ma’aikatar ilimi

Tsohon gwamnan na Kano ya bayyana cewa haɗin gwiwarsa da Obi a zaɓen 2027 wani sabon mataki ne na samar da ci gaba a Najeriya.

Ya kuma bayyana cewa shugabannin NDC sun cimma matsaya cewa idan suka samu nasarar lashe zaɓen, shi zai jagoranci ma’aikatar ilimi ta ƙasa.

Kwankwaso ya ce Obi ya amince da wannan matsaya ne bayan ya gabatar masa da tsarin inganta ilimi da ya aiwatar a lokacin da yake gwamnan Kano.

Kwankwaso ya fadi abin da Tinubu ke tsoro

Mun ba ku labarin cewa mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Rabiu Kwankwaso, ya zargi gwamnatin Tinubu kan dokokin haraji.

Kwankwaso ya yi gargaɗin cewa idan APC ta sake samun nasara, 'yan Najeriya za su iya fuskantar ƙarin nau'ukan karɓar haraji.

Ya ce idan NDC ta samu amanar 'yan Najeriya, za ta soke harajin da ta kira marasa amfani tare da samar da ingantaccen ilimi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.