Sakon Tinubu ga Shugaban Nijar, Tchiani bayan Rasuwar Mahaifinsa
- Shugaba Bola Tinubu ya miƙa ta'aziyyarsa ga shugaban mulkin sojan Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, kan rasuwar mahaifinsa
- Elhadji Tiani Hassane ya rasu ne a ranar Alhamis, 5 ga Nuwambar 2026, yana da shekara 110 a duniya
- Tinubu ya tabbatar wa gwamnatin Nijar cewa Najeriya na tare da ita a wannan lokaci na jimami
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa saƙon ta'aziyya ga shugaban mulkin sojan Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, bisa rasuwar mahaifinsa, Elhadji Tiani Hassane.
Mahaifin shugaban Nijar ya rasu ne a ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwambar 2026, yana da shekara 110 a duniya.

Source: Facebook
A cikin saƙon ta'aziyyar, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya da al'ummar Najeriya na tare da gwamnatin Nijar da al'ummarta a wannan lokaci na jimami.
Shugaban ya ce rasuwar uba na haifar da babban alhini da ba ya misaltuwa, amma ya kamata Janar Tiani ya samu kwanciyar hankali bisa la'akari da irin tasirin da mahaifinsa ya yi a rayuwar al'ummarsa.
Tinubu ya bayyana cewa mahaifin shugaban Nijar ya bar kyakkyawan tarihi na imani, mutunci da gaskiya, tare da rayuwa mai albarka wadda ta kai shekara 110.
Ya ce:
“Rasuwar uba na haifar da babban alhini mai zurfi da kuma raɗaɗi na musamman, ina fatan za ku samu kwanciyar hankali bisa la'akari da irin tasirin da mahaifinsa ya yi a rayuwar al'ummarsa, da kuma yadda ya rayu har ya kai shekara 110.
“A wannan lokaci na jimami, ina addu'ar za ka samu kwanciyar hankali daga kyakkyawan tarihin imani, mutunci da gaskiya da mahaifinka ya bari, tare da sanin cewa tsawon rayuwarsa mai albarka ya kasance abin ni'ima ga duk waɗanda suka san shi.
“Najeriya na tare da Mai Girma, da gwamnatin Jamhuriyar Nijar da al'ummarta a wannan lokaci na jimami.”
Shugaban ya ƙara da cewa Najeriya na nuna cikakken goyon baya da tausayawa ga shugaban Nijar, gwamnatinsa da al'ummarta a wannan lokaci na jimami.
A ƙarshe, Tinubu ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da ya jiƙan marigayin, ya ba shi Aljannatul Firdausi, sannan ya ba iyalansa da sauran waɗanda ya bari haƙurin jure wannan rashi.
Karin bayani na tafe....
Asali: Legit.ng

