Indonesia: An Yi wa Shugaban Kasa Kutse a Waya, An Saurari Maganganun da Yake Yi

Indonesia: An Yi wa Shugaban Kasa Kutse a Waya, An Saurari Maganganun da Yake Yi

  • ’Yan sanda sun kama mutane uku bisa zargin kutse da sauraron kiran wayar Shugaban kasar Indonesia, Prabowo Subianto da wasu manyan mutane
  • Ministan Shari’a na kasar ya bayyana cewa ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin babban janar ne a rundunar sojin Indonesia
  • Idan aka same su da laifi, za su iya fuskantar hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara 10

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Indonesia - Hukumomin Indonesia sun kama mutane uku bisa zargin kutse da sauraron kiran wayar shugaban kasa, Prabowo Subianto, kamar yadda ’yan sanda suka bayyana a ranar Talata.

Prabowo, wanda ya kama mulki a 2024, na fuskantar matsin lamba a kan yadda gwamnatinsa ke tafiyar da tattalin arziki da kuma yadda take magance gobarar daji da ta yi barna a ƙasar da ke yankin Kudu maso Gabashin Asiya.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya kamata ku sani game da tallafin N50,000 da aka fara turawa mutane a Najeriya

Prabowo Subianto.
Shugaban kasar Indonesia, Prabowo Subianto yana jawabi shekara-shekara kan halin da kasa ke ciki gabanin ranar samun yancin kai ranar 14 ga Agusta, 2026 Hoto: BAY ISMOYO
Source: Getty Images

Channels tv ta ruwaito cewa rahotannin kafafen yaɗa labarai sun nuna cewa ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin na iya kasancewa wani babban jami’in gwamnati.

Yan sanda sun kama mutum 3

Babban jami’in binciken laifuka, Asep Safrudin, ya bayyana sunayen waɗanda ake zargin da baƙaƙen haruffa kawai, wato LSP, ASN da EH.

Ya ce ana gudanar da bincike a kansu bisa zargin kutse da sauraron "wayar Shugaban Jamhuriyar Indonesia” da kuma ta wasu fitattun mutane.

Sauran waɗanda ake zargin an kutsa cikin layukan wayoyinsu sun haɗa da jami’an gwamnati, ’yan siyasa, ’yan jarida, wakilan ƙungiyoyi masu zaman kansu (NGOs) da ’yan kasuwa.

Ana zargin sun saurari maganganu

A cewar Asep, an saurari wayoyin mutanen, ciki har da ta Shugaba Prabowo, “ba tare da wani sahihin dalili na doka ba, ko kuma bin matakan bincike da gudanar da binciken farko kamar yadda dokokin ƙasar suka tanada ba”.

Asep ya shaida wa manema labarai a Jakarta cewa wani jami’in ɗan sanda da ya samu labarin zargin aikata laifin ne ya shigar da ƙara a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Ciyaman ya sha da ƙyar da miyagun yan daba suka farmaki wurin zaɓen fitar da gwanin APC

Tun daga lokacin, ’yan sanda sun yi hira da shaidu 10 da ƙwararru uku, tare da ƙwace wasu kayayyakin da suka haɗa da wayoyin hannu guda 11, kwamfuta ta iPad da na’urorin ajiya na bayanai guda huɗu (flash drives).

Idan aka same su da laifi, waɗanda ake zargin za su iya fuskantar hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara 10, kamar yadda NST Online ta ruwaito.

Waya.
Wani matashi rike da wayarsa yana duba taswira Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An ambaci babban janar a cikinsu

A wani taron manema labarai na daban, Ministan Shari’a, Yusril Ihza Mahendra, ya bayyana cewa LSP janar ne da ke aiki a halin yanzu.

Kafofin yaɗa labaran Indonesiya sun ce ana kyautata zaton LSP ɗin shi ne Listyo Sigit Prabowo, wanda ba shi da alaƙa da Shugaba Prabowo.

An naɗa Listyo a matsayin shugaban ma’aikatan shugaban ƙasa kimanin wata guda da ya gabata, bayan ya shafe shekara biyar yana riƙe da muƙamin babban sufeton ’yan sandan ƙasar.

Shugaban Bangladesh ya yi murabus

Kun ji cewa shugaban Bangladesh, Mohammad Shahabuddin, ya yi murabus shekaru kadan bayan kotu ta samu tsohuwar Firaminstan kasar da laifi.

Wannan na zuwa ne a lokacin da ake rade-radin akwai wata alaka mai karfi tsakaninsa da tsohuwar Firaminsta, Sheikh Hasina da aka kora bayan zanga-zanga a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262