Matasa Sun Hargitsa wajen da Shettima Ya Je Kamfe Din APC na 2027

Matasa Sun Hargitsa wajen da Shettima Ya Je Kamfe Din APC na 2027

  • Gwamnatin Nasarawa ta umarci DSS ta gudanar da cikakken bincike kan rikicin da ya faru yayin ziyarar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ga Sarkin Lafia
  • Gwamnatin ta zargi wasu matasa da hannu a lamarin, tana mai cewa ana zargin sun yi hakan ne domin ɓata sunan gwamnatin jihar da al'ummarta
  • Rahotanni sun ce akalla mutum 40 sun jikkata, yayin da wasu da dama suka ɓace bayan rikicin da ya ɓarke a wajen gangamin APC a Lafia

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Lafia, Nasarawa – Gwamnatin jihar Nasarawa ta umarci hukumar DSS da ta gudanar da bincike kan rikicin da ya kawo cikas ga ziyarar girmamawa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kai wa Sarkin Lafia ranar Laraba.

An bayyana umarnin ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin jihar Nasarawa, Dr Shuaibu Magaji Labaran, ya sanya wa hannu.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya fito yana murna da rusa takarar Atiku da dukkan 'yan ADC a Najeriya

Kashim Shettima a taron APC a Nasarawa
Kashim Shettima da wasu mataa a taron APC. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa Shettima ya kai ziyarar ne bayan halartar gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC a Lafia, inda ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Wadanda ake zargi kan rikicin

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta yi matuƙar baƙin ciki kan yadda wasu matasa da ta bayyana a matsayin masu fusata suka kawo cikas ga ziyarar girmamawar.

Sanarwar ta ce ana zargin matasan na da alaƙa da wasu manyan mutane, ciki har da Sanata Umaru Tanko Al-Makura da tsohon Sufeto Janar na 'yan sanda, Mohammed Abubakar Adamu.

Gwamnatin ta zargi waɗanda suka aikata lamarin da yunƙurin ɓata sunanta da na al'ummar jihar Nasarawa.

An umarci DSS ta gano su

Gwamnatin Nasarawa ta bayyana cewa ba za ta amince da duk wani mataki da zai nuna rashin girmamawa ga hukumomin da kundin tsarin mulki ya kafa ba, musamman ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa.

Ta ce an umarci DSS da ta fara cikakken bincike cikin gaggawa domin gano musabbabin rikicin, waɗanda suka aikata shi da kuma waɗanda suka ɗauki nauyinsa.

Kara karanta wannan

2027: Sarkin Musulmi ya gana da Atiku da manyan ADC a Sokoto

Taswirar jihar Nasarawa
Taswirar jihar Nasarawa a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Sanarwar ta ƙara da cewa za a gurfanar da duk waɗanda aka samu da hannu a lamarin domin su fuskanci hukunci bisa tanadin doka.

Gwamnatin ta kuma yi kira ga al'ummar jihar da su ci gaba da bin doka da oda yayin gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Akalla mutum 40 sun jikkata

Premium Times ta wallafa cewa akalla mutum 40 sun samu raunuka, yayin da wasu da dama suka ɓace sakamakon rikicin da ya ɓarke a wajen gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Lafia.

Lamarin ya jawo damuwa a jihar, musamman ganin yadda rikicin ya faru a yayin wani babban taron siyasa da manyan jami'an gwamnati suka halarta.

An yi rikici a taron APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa an samu ɗan tashin hankali a wajen gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Lafia, jihar Nasarawa.

Hakan na zuwa ne bayan magoya bayan ɗan takarar gwamnan SDP, tsohon Sufeto Janar na 'yan sanda Mohammed Abubakar Adamu, sun yi kirarin goyon bayansa.

Gwamna Abdullahi Sule ne ya fara jagorantar kirarin “Sai Wadada” domin nuna goyon baya ga ɗan takarar APC, Sanata Ahmed Aliyu Wadada, amma magoya bayan Adamu suka mayar da martani da kirarin “Sai IG”.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng