Buhari zai kaddamar da aikin titin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi ranar Talata

Buhari zai kaddamar da aikin titin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi ranar Talata

- Gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan aikin layin dogo daga Kano zuwa jamhuriyar Nijar

- Ministan sufuri na kasa ya sanar da za a fara aikin a ranar Talata mai zuwa a shafinsa na Twitter

- Aikin layin dogon an bayyana zai shafi wasu garuruwan jihar Katsina, Jigawa da kuma na jihar Kano

A ranar Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari zai yi bikin aza tubalin ginin layin dogo daga Kano zuwa Maradi, wanda aka bayar a kan dala biliyan biyu, Daily Trust ta ruwaito.

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, wanda ya sanar da haka ta shafinsa na twitter, ya ce za a bude aikin ne a yankin Katsina.

A watan Janairun 2021, Gwamnatin Tarayya ta shiga yarjejeniyar aiki tare da Kamfanin Mota-Engil kan aikin layin dogo tsakanin Kano zuwa Maradi da zai ci dala biliyan 1.959.

KU KARANTA: Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya dawo kan kafofin sada zumunta

Buhari zai kaddamar da aikin titin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi ranar Talata
Buhari zai kaddamar da aikin titin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi ranar Talata Hoto: Oyo Gist
Source: UGC

Amaechi ya sanya hannu a madadin Gwamnatin Tarayya yayin da manajan darakta na Mota-Engil, Antonio Gvoea, ya sanya hannu a madadin kamfanin.

Ana sa ran aikin layin dogo zai hade jihohi uku na arewacin Najeriya - Kano, Katsina da Jigawa sannan ya kare a Maradi, Jamhuriyar Nijar.

Sauran garuruwan da layin jirgin kasan zai shafa a Najeriya sun hada da Danbatta, Kazaure, Daura, Mashi, Katsina da Jibiya.

An kayyade lokacin aikin cikin watanni 36.

KU KARANTA: Kasuwancin kiwon shanu ya fi na kudin intanet, in ji Adamu Garba

A wani labarin, Majalisar zartarwa ta tarayya, FEC, a ranar Laraba, ta amince da kafa karin jami’o’i 20 masu zaman kansu a kasar.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa amincewar ta biyo bayan wani rubutu da Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya gabatar yayin taron yau wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Tara daga cikin jami’o’i masu zaman kansu suna Arewa maso Tsakiya, uku a Kudu maso Kudu, biyu a Kudu maso Gabas, biyar daga cikinsu a Arewa maso Yamma da kuma daya a Kudu maso Yamma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel