Obansajo Ya Bayyana Manyan Shugabannin da Suka Yi Barazanar Kashe Abacha
- Obasanjo ya ce marigayi Janar Sani Abacha ya shirya kashe shi tare da Janar Shehu Yar’Adua da MKO Abiola lokacin da yake tsare a gidan yari
- Ya bayyana cewa tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter ya ziyarci Najeriya domin roƙon Abacha ya ƙyale shi, yayin da James Callaghan ya yi barazana gare shi
- Tsohon shugaban ƙasar ya ce addu’a da yardar Allah sun taimaka masa ya tsira, sannan ya yi gargaɗi kan tura yara zuwa fagen daga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya bayyana yadda ya kusa rasa ransa a lokacin da yake tsare a gidan yari ƙarƙashin mulkin soja na marigayi Janar Sani Abacha.
Obasanjo ya ce sa hannun wasu shugabannin ƙasashen duniya da kuma dagewarsa wajen yin addu'a sun taimaka wajen kuɓutar da shi daga shirin kashe shi.

Source: Twitter
Ya bayyana hakan ne da harshen Yarbanci a wani taron gabatar da littafi da aka gudanar a Jami'ar Ibadan da ke Jihar Oyo. Tashar BBC Yoruba ce ta wallafa faifan bidiyon da ke ɗauke da bayanan tsohon shugaban ƙasar.
Abacha ya shirya kashe Obasanjo da wasu
Obasanjo ya ce Abacha ya riga ya yanke shawarar kashe shi tare da wasu fitattun ’yan Najeriya guda biyu, wato marigayi Janar Shehu Yar’Adua da Cif Moshood Kashimawo Abiola.
Abiola shi ne wanda aka amince da cewa ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga Yuni, 1993, wanda aka soke.
Tsohon shugaban ƙasar ya ce Abacha ya taɓa bayyana wannan shiri ga marigayi attajirin nan kuma mai taimakon jama'a daga Ibadan, Cif Alao Arisekola.
Da yake magana kan Arisekola da Abacha, Obasanjo ya ce:
“Allah ya ji ƙan shi, amma dangane da Abacha, Allah zai iya ji ƙansa idan shi ma yana so.”
Obasanjo, wanda ya taɓa mulkar Najeriya a matsayin shugaban ƙasa na soja kafin daga baya ya dawo kan mulki ta hanyar zaɓen dimokuraɗiyya, ya ce ya tsira ne sakamakon wasu abubuwa na musamman.
Yadda shugabannin ƙasashen duniya suka shiga tsakani
Obasanjo ya bayyana cewa tsohon shugaban Amurka na 39, Jimmy Carter, ya zo Najeriya da kansa domin tattaunawa da Abacha a madadinsa.
Ya kuma ce tsohon firaministan Birtaniya, James Callaghan, ya ɗauki mataki mai tsauri wajen ƙoƙarin hana Abacha kashe shi.
A cewar Obasanjo, Callaghan ya gargaɗi Abacha cewa shi ma zai fuskanci kisa idan ya aiwatar da shirin kashe tsohon shugaban ƙasar.
Wannan shiga tsakani na shugabannin ƙasashen duniya ya taimaka wajen ƙara matsin lamba kan gwamnatin Abacha game da makomar Obasanjo.
Obasanjo ya danganta tsirarsa da addu'a
Baya ga taimakon diflomasiyya, Obasanjo ya ce dagewarsa wajen yin addu'a a lokacin da yake tsare na daga cikin abubuwan da suka taimaka masa ya tsira.
Ya bayyana kansa a matsayin mutum mai yawan addu'a a lokacin da yake gidan yari, yana mai cewa sai da yardar Allah ya samu damar fita da rai.
A cewarsa, duk da haɗarin da yake fuskanta a lokacin, ya ci gaba da dogaro da addu'a har zuwa lokacin da ya samu 'yanci.

Source: Facebook
Amaechi ya yi zargi kan Obasanjo
A wani labarin kuma, kun ji cewa Rotimi Amaechi, ya bayyana yadda barazanar kama shi da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi ta tilasta masa barin Najeriya zuwa Ghana a lokacin da yake fafutukar zama gwamnan jihar Rivers.
Amaechi ya ce Obasanjo ya yi ƙoƙarin hana shi zama gwamnan Rivers, inda ya bayyana cewa ya bar Najeriya ne bayan tsohon shugaban ƙasar ya yi barazanar sa a gaba a kama shi.
Asali: Legit.ng


