Nafiu Bala Ya Fitar da Sanarwa ga Shugabannin ADC bayan Rusa Takarar Atiku
- Tsagin am’iyyar ADC ta umarci shugabanninta na ƙananan hukumomi da jihohi su tattara tare da miƙa sunayen mambobinta
- Shugabannin jam’iyyar na jihohi za su miƙa kundin sunayen mambobin kafin ko a ranar Alhamis, 12 ga Nuwamba, 2026
- Nafiu Bala ya kuma buƙaci ’yan takarar tsaginsa su ci gaba da kamfen duk da barazanar da ya ce wasu 'yan siyasa na yi masu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugabancin tsagin jam’iyyar ADC ya ba shugabannin jam’iyyar a matakin jihohi wa’adin zuwa ranar Alhamis, 12 ga Nuwamba, 2026, domin miƙa kundin sunayen mambobin jam’iyyar zuwa Abuja.
A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ranar Lahadi, 8 ga Nuwamba, 2026 ta bayyana matakan da shugabannin mazabu, ƙananan hukumomi da jihohi za su bi wajen tattara da miƙa bayanan mambobinta.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai game da umarnin ne a wani sako da shugaban tsagin jam'iyyar, Nafiu Bala ya wallafa a shafinsa na Facebook.
ADC ta tsara tattara mambobinta
Nafiu Bala ya umarci dukkan shugabannin mazabu da ke faɗin Najeriya su miƙa kwafin kundin sunayen mambobinsu ga shugabannin jam’iyyar na ƙananan hukumominsu.
Bayan karɓar bayanan, shugabannin ƙananan hukumomi za su tattara su wuri guda kafin su miƙa su ga sakatarorin jam’iyyar na jihohi domin aikawa da su hedikwatar ƙasa.
ADC ta kuma umarci shugabannin jam’iyyar na jihohi su tabbatar an miƙa dukkan bayanan da aka tattara zuwa sakatariyar ƙasa kafin ko a ranar Alhamis, 12 ga Nuwamba.
Shugabancin ADC ya bayyana cewa dukkan kundin sunayen mambobin da aka tattara a jihohi za a miƙa su ne zuwa sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa da ke lamba 4, Miriam Ikejiani Clarke Crescent, unguwar Guzape, Abuja.

Source: Original
ADC ta yi magana kan kamfen
A cikin sanarwar, jam’iyyar ta buƙaci dukkan ’yan takararta a matakai daban-daban su ci gaba da kamfen tare da ƙara ƙaimi wajen neman goyon bayan jama’a.
Ta ce jinkirin isar da hukuncin kotu bai kamata ya ɗauke hankalin ’yan takara daga ayyukan da suke yi ba, musamman saboda barazanar da ta ce ƙungiyar haɗaka ke yi musu.
Jam’iyyar ta bayyana cewa ya kamata ’yan takararta su mayar da hankali kan ayyukansu a fagen siyasa, tare da nuna godiya ga hukuncin kotu ta hanyar ƙara ƙaimi wajen gudanar da kamfen.
APC ta yi magana kan rikicin ADC
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam’iyyar APC ta buƙaci ɓangaren ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark ya magance rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar.
Jam'iyyar APC ta ce ba ta da hannu a shari’ar da ta kai ga tsige shugabancin ɓangaren Mark, tana mai cewa rikicin na cikin gida ne na ADC.
Jam’iyyar mai mulki ta kuma zargi David Mark da abokan tafiyarsa da karɓe ikon ADC domin biyan buƙatar Atiku Abubakar ta neman shugabancin Najeriya.
Asali: Legit.ng

