Kwankwaso Ya Bayyana Abin da Tinubu Yake Tsoro kan Zaben 2027
- Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Rabiu Kwankwaso, ya zargi gwamnatin Tinubu kan dokokin haraji
- Kwankwaso ya yi gargaɗin cewa idan APC ta sake samun nasara, 'yan Najeriya za su iya fuskantar ƙarin nau'ukan karɓar haraji
- Ya ce idan NDC ta samu amanar 'yan Najeriya, za ta soke harajin da ta kira marasa amfani tare da samar da ingantaccen ilimi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Jigawa - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar National Democratic Congress (NDC), ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jinkirta karɓar haraji bisa sababbin dokokin haraji.
Kwankwaso ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya ta ɗauki wannan mataki ne saboda fargabar cewa aiwatar da dokokin na iya jawo mata matsala a babban zaɓen 2027.

Source: Twitter
Ya bayyana hakan ne yayin bikin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen NDC a Jihar Jigawa, wanda aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Dalilin da ya sa gwamnati ta jinkirta karɓar harajin
Kwankwaso ya ce duk da cewa an amince da ƙudurin dokokin sauya tsarin haraji tare da mayar da su doka, gwamnatin tarayya na nuna jinkirin fara aiwatar da su.
A cewarsa, gwamnati na fargabar cewa fara karɓar harajin zai iya shafar damar jam'iyyar APC ta sake samun nasara a zaɓen 2027.
"An riga an amince da ƙudurin dokar, amma yanzu gwamnatin tarayya tana tsoron shan kaye a zaɓe. Wannan ne ya sa ta jinkirta karɓar harajin.” In ji shi.
Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasar ya yi gargaɗin cewa 'yan Najeriya za su iya fuskantar ƙarin nau'ukan karɓar haraji idan APC ta sake samun nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa.
“Da zarar sun samu dama ta biyu, Allah Ya kiyaye, 'yan Najeriya za su sha wahala sakamakon nau'ukan karɓar haraji daban-daban. Za su riƙa zuwa gida-gida, har su duba ƙarƙashin gadon mutane domin karɓar haraji.” In ji shi.

Kara karanta wannan
Okowa: Abokin takarar Atiku a 2023 ya bayyana dalilin da ya sa suka raba gari ya koma APC
Kwankwaso ya yi zargi kan Sanatan Kano
Kwankwaso ya kuma yi zargin cewa wani ɗan Kano ne ya jagoranci zaman da aka gudanar domin amincewa da ƙudurin dokokin harajin.
Ya ce shugaban Majalisar Dattawa ma ya ƙi halartar zaman da gangan saboda ba ya son a danganta shi da amincewa da dokokin.
A kalamansa:
“Abin da ya fi muni shi ne, ɗaya daga cikinmu daga Kano ne ya jagoranci zaman amincewa da ƙudurin dokar harajin. Hatta shugaban Majalisar Dattawa ya ƙi zuwa da gangan saboda ba ya son ya kasance cikin lamarin.”
Abin da NDC ta yi wa 'yan Najeriya alƙawari
Kwankwaso ya ce jam'iyyar NDC ta shiga siyasa ne domin kare muradun 'yan Najeriya, inda ya yi alƙawarin cewa za ta soke harajin da ta ɗauka ba su da amfani idan aka ba ta damar mulki.
Ya kuma yi alƙawarin cewa jam'iyyar za ta samar da ingantaccen ilimi tare da ɗaukar nauyin karatun yara.
Ya buƙaci 'yan Najeriya da kada su sake bai wa APC damar mulki, yana mai cewa sake zaɓen jam'iyyar zai iya jefa makomar ƙasar cikin haɗari.

Kara karanta wannan
2027: Shugaban majalisa ya bayyana abin da ya zama dole ga 'yan Najeriya kan Tinubu

Source: Facebook
NDC ta yi zargi kan NDC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta yi zarge-zarge kan jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Jam'iyyar NDC ta zargi APC da matsa wa wasu otal-otal a Abuja lamba domin hana jam’iyyar adawa amfani da wurarensu wajen gudanar da taruka.
Asali: Legit.ng
