Zaɓi 2 da Suka Rage wa Atiku bayan Rushe Takararsa, Shugabannin ADC
- Hukuncin babbar kotun tarayya ya jefa burin Atiku Abubakar na neman shugabancin Najeriya a 2027 cikin sabon ƙalubale
- Masana shari'a sun bayyana cewa ɗaukaka ƙara ce hanya mafi dacewa da Atiku zai bi domin ƙalubalantar hukuncin kotun
- Sauya sheƙa zuwa wata jam'iyya na daga cikin zaɓuɓɓukansa, amma dokar zaɓe na iya hana shi samun takara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Burin Atiku Abubakar, na sake neman shugabancin ƙasar a zaɓen 2027 ya fuskanci sabon tarnaki bayan kotu ta soke takararsa ƙarƙashin jam'iyyar ADC.
Hukuncin da mai shari'a Peter Lifu ya yanke a ranar Alhamis ya bayyana cewa kwamitin riƙon ƙwarya na jam'iyyar ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark bai samu halastacciyar damar gudanar da ayyukansa ba.

Source: Twitter
Kwamitin ne ya shirya zaɓen fitar da gwani da ya ba Atiku tikitin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar, cewar Punch.
Korafin da Nafiu Bala ke yi
Nafiu Bala Gombe ne ya kai ƙarar kotu, inda ya nemi a binciki sahihancin yadda David Mark ya karɓi shugabancin riƙon ƙwarya na ADC.
Sai dai hukuncin ya zo ne a lokacin da jam'iyyar da Atiku suka fara ƙarfafa ayyukan yaƙin neman zaɓensu a jihar Sokoto.
Yanzu haka dai hankula sun koma kan matakan da Atiku zai iya ɗauka domin ci gaba da burinsa na shiga takarar shugaban ƙasa.
1. Ɗaukaka ƙara ita ce hanya mafi sauƙi
Ɗaya daga cikin matakan da Atiku zai iya ɗauka shi ne kai ƙarar zuwa kotun ɗaukaka ƙara domin neman a sake duba hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke.
Masanin shari'a El-Zubair Abubakar ya bayyanawa BBC Hausa cewa wannan ita ce hanyar da tsohon mataimakin shugaban ƙasar da jam'iyyar ADC za su iya bi a halin yanzu.
A cewarsa, idan kotun ɗaukaka ƙara ta dakatar da aiwatar da hukuncin, hakan zai ba Atiku da ADC damar ci gaba da shirye-shiryensu na siyasa yayin da ake ci gaba da shari'ar.
Masanin ya jaddada cewa ya kamata ɓangaren Atiku ya bi hanyoyin doka domin neman haƙƙinsa maimakon shiga wata takaddama.

Source: Twitter
2. Sauya sheƙa zuwa wata jam'iyyar siyasa
Wata hanyar da Atiku zai iya tunani a kanta ita ce barin ADC domin komawa wata jam'iyyar da za ta ba shi damar neman tikitin takarar shugaban ƙasa.
Sai dai masanin shari'a Audu Bulama Bukarti ya yi gargaɗin cewa sauya jam'iyya a wannan lokaci ba zai ba Atiku damar shiga takarar shugaban ƙasa ba.
Ya bayyana cewa duk da cewa dokar Najeriya ta bai wa 'yan siyasa damar sauya jam'iyya a kowane lokaci, akwai sharuɗɗan da dole ne su cika kafin samun damar takara.
Sashe na 77 na dokar zaɓen Najeriya ya tanadi cewa dole ne mai neman takara ya kasance ɗan jam'iyya na tsawon kwanaki 30 kafin gudanar da zaɓen fitar da gwani.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC, ta tsara gudanar da zaɓen fitar da gwani daga ranar 23 ga Afrilu zuwa 30 ga Mayun 2027.
Wannan na nufin duk wanda yake son neman takara dole ne ya shiga jam'iyyar da yake son wakilta kafin cikar wa'adin da dokar ta tanada.

Kara karanta wannan
2027: Yadda mutane suka riƙa rera 'Tinubu must go' yayin tarbar Atiku ya ja hankali
Asalin rikicin da ya dabaibaye ADC
Matsalar shugabancin ADC ta samo asali ne a shekarar 2025 lokacin da wasu manyan 'yan siyasa suka fara komawa jam'iyyar domin gina haɗakar da za ta kalubalanci APC a zaɓen 2027.
Daga cikin fitattun mutanen da suka koma ADC akwai Atiku Abubakar, David Mark, Rauf Aregbesola, Nasir El-Rufai da Rotimi Amaechi.
Bayan murabus ɗin tsoffin shugabannin jam'iyyar ƙarƙashin Ralph Nwosu, David Mark ya karɓi shugabancin riƙon ƙwarya a ranar 29 ga Yulin 2025.
Sai dai Nafi'u Bala Gombe, wanda ya taɓa kasancewa mataimakin shugaban jam'iyyar, ya ƙi amincewa da sauyin shugabancin, yana mai cewa bai yi murabus daga matsayinsa ba.
Daga nan ne ya shigar da ƙara domin neman kotu ta amince da shi a matsayin shugaban ADC na gaskiya.
Obi ya shiga wa Atiku fada
An ji cewa dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi ya nuna damuwa kan hukuncin kotu da ta soke zaɓen Atiku Abubakar a matsayin dan takarar ADC.
Obi ya ce hukuncin na iya jawo rashin tabbas ga jam’iyyun adawa gabanin zaɓe, tare da shafar damar masu zaɓe wajen zaɓar shugabannin da suke so.
Asali: Legit.ng

