Ana Batun N50,00, Tinubu Ya Kawo Sabon Shirin Tallafin Naira Miliyan 100
- Hukumar SMEDAN ta ƙaddamar da shirin da ke da burin samar da hamshakan ’yan kasuwa 100 ta hanyar horo da tallafin kuɗi
- Shirin zai haɗa da gasar gabatar da dabarun kasuwanci da kyautar Naira miliyan 100, domin tallafa wa ƙananan ’yan kasuwa
- An ce za a raba tallafin a taron GROW Nigerian na shekarar 2026 da kuma wani taro da za a gudanar a Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Lagos – Hukumar bunƙasa ƙananan da matsakaitan masana’antu da ’yan kasuwa ta Najeriya (SMEDAN) ta ƙaddamar da shirin tallafa wa ’yan kasuwa 100 domin su zama masu manyan jarin kasuwanci, ta hanyar horaswa da tallafin kuɗi.
Shirin na daga cikin ƙoƙarin hukumar na magance matsalolin ƙarancin kuɗaɗen gudanar da kasuwanci da kuma rashin ƙwarewar da ke hana ƙananan ’yan kasuwa bunƙasa harkokinsu.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa za a gudanar da shirin ne a ƙarƙashin taron GROW Nigerian na 2026 da za a yi a birnin Lagos, inda za a haɗa horas da mahalarta da tallafin kuɗi da kuma damar samun kasuwanni.
Za a bayar da Naira miliyan 100
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Alhamis, ta bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan abubuwan da za a gudanar a taron shi ne gasar da aka ware mata kyautar Naira miliyan 100.
Gasar za ta bai wa ’yan kasuwa masu kyawawan dabarun kasuwanci damar gabatar da shirye-shiryensu domin samun tallafin da zai taimaka musu wajen bunƙasa harkokinsu.
Sanarwar ta ƙara da cewa za a raba kuɗaɗen tallafin a taron da kuma wani taro da za a gudanar a Arewacin Najeriya, yayin da aka tsara gabatar da sakamakon ƙarshe da bayar da kyaututtuka a ranar 10 ga watan Nuwamba.
SMEDAN ta bayyana dalilin shirin
Shugaban hukumar SMEDAN, Charles Odii, ya ce an ƙirƙiri shirin ne domin cike gibin da ke tsakanin ƙwarewar gudanar da kasuwanci da kuma samun kuɗin da ake buƙata wajen farawa ko faɗaɗa harkokin kasuwanci.
Odii ya bayyana cewa akwai ’yan Najeriya da dama masu ƙwarewa da dabarun kasuwanci, amma rashin jari da ilimin sarrafa kasuwanci na hana su mayar da waɗannan dabaru zuwa sana’o’in da za su dore.

Source: Original
Tribune ta rahoto ya ce samun kuɗin sayen kayan aiki na iya sauya makomar wanda ya koyi sana’a amma ba shi da abin da zai fara aiki da shi.
Shugaban hukumar ya kuma bayyana cewa ilimin tsara farashi, jawo kwastomomi da sarrafa kuɗaɗen kasuwanci na taimaka wa ’yan kasuwa wajen samun ci gaba mai ɗorewa.
Yadda ake tura N50,000
A wani labarin, kun ji cewa kamfanin hada-hadar kuɗi na Moniepoint ya fitar da ƙarin bayani kan yadda waɗanda suka cancanci tallafin Naira 50,000 na gwamnatin tarayya za su karɓi kuɗinsu.
Kamfanin ya bayyana cewa waɗanda suka samu saƙon waya na sanar da biyan tallafin za su yi amfani da lambar USSD da aka aika masu domin amincewa da karɓar kuɗin.
Moniepoint ta kuma yi bayani kan matakin da mutum zai ɗauka idan ya samu saƙon kuskure yayin amfani da lambar *5573*27#, tare da bayyana lokacin da ake sa ran kuɗin zai shiga.
Asali: Legit.ng


