Yadda Fasto Ya Mayar da Bilioyoyi ga EFCC bayan Samunsu a Cocinsa

Yadda Fasto Ya Mayar da Bilioyoyi ga EFCC bayan Samunsu a Cocinsa

  • Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana yadda Fasto Enoch Adeboye ya umarci a mayar da biliyoyin kuɗin da aka gano sun shiga ayyukan RCCG
  • Olukoyede ya ce Adeboye ya fusata bayan an sanar da shi cewa kuɗaɗen da ake zargin an samo su ta hanyar aikata laifukan kuɗi sun shiga cocin
  • Shugaban EFCC ya gargaɗi shugabannin coci kan bai wa masu kuɗin haramun matsayi da daraja tare da musayar kuɗi domin samun mukaman addini

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja- Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana yadda Fasto Enoch Adeboye ya bayar da umarnin mayar da biliyoyin kuɗin da aka gano sun shiga wasu ayyukan Cocinsa.

Olukoyede ya ce Fasto Adeboye ya ɗauki matakin ne bayan hukumar EFCC ta sanar da shi cewa an gano wasu kuɗaɗen da ake zargin an samu ta hanyar aikata laifukan kuɗi a cikin ayyukan cocin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya ta faɗi yankuna da jihohin da su ci moriyar tallafin N50,000

Fasto Adeboye ya yi abin a yaba
Fasto Enoch Adeboye yayin da yake huduba a cocinsa. Hoto: Enoch Adeboye.
Source: Facebook

Shugaban EFCC ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ya gudanar da ma'aikatan coci da ministocinta bayan kammala shirin Holy Ghost Service na wata-wata a Redemption City of God da ke Simawa, jihar Ogun, cewar Vanguard.

Taron wanda aka gudanar bisa gayyatar Fasto Adeboye, ya samu taken, "Ka'idojin ɗabi'a da yaƙi da cin hanci a cikin al'ummar Kiristoci."

Yadda Adeboye ya umarci a mayar da kuɗin

Da yake bayanin yadda lamarin ya faru, Olukoyede ya ce wani mutum da hukumar ke bincike a kansa ya gudanar da hada-hadar kuɗi ta biliyoyin naira, inda aka gano wasu daga cikin kuɗaɗen sun shiga ayyukan RCCG.

Ya bayyana cewa da kansa ya je wajen Fasto Adeboye domin sanar da shi sakamakon binciken hukumar, amma malamin ya fusata sosai bayan jin bayanin.

Olukoyede ya ce Adeboye ya kira wasu fastoci tare da umartar su da su tabbatar da mayar da duk kuɗaɗen da aka gano cikin awa 24.

Kara karanta wannan

An bayyana tulin ayyukan alherin Tinubu a Arewa da ya cancanci tazarce a 2027

A cewarsa:

"Fuskar Daddy ta nuna kamar na zargi kaina da kai masa wannan batu. Ya fusata sosai. Ya kira fastoci ɗaya ko biyu sannan ya ce musu, na ba ku awa 24.
Duk abin da kuka gano cewa wannan mutumin da ake tuhuma ya shigar cikin RCCG, ku mayar da shi cikin awa 24."

EFCC ya ba da labarin tsare faston RCCG

A wani ɓangare na jawabin nasa, Olukoyede ya bayyana cewa ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi ba shi baƙin ciki a rayuwarsa shi ne lokacin da ya bayar da umarnin tsare wani babban fasto a RCCG.

Ya ce duk da matsayin faston a cocin, bai da wani zaɓi face amincewa da tsare shi saboda zargin laifukan kuɗi da ya aikata a wurin aikinsa na yau da kullum.

Ya jaddada cewa zargin bai shafi ayyukan faston a cikin coci ba, sai dai abin da ya aikata a wajen hidimarsa ta addini.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya kamata ku sani game da tallafin N50,000 da aka fara turawa mutane a Najeriya

Adeboye ya nemo mafita kan tsaro

Kun ji cewa Fasto Enoch Adeboye ya bayyana cewa tun da aka fara kashe kiristoci a Najeriya, ya ankarar da shugabannin kasar don daukar mataki.

Babban limamin cocin RCCG ya shawarci Shugaba Tinubu ya dauki matakan gaggawa tun kafin Amurka ta fara kawo hari.

A cewarsa, ya kamata Tinubu ya ba hafsoshin tsaro wa'adin watanni uku su kawar da yan ta'adda ko kuma su yi murabus.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.