Marasa Lafiya na Shanye a Asibiti, an Kama Likitoci na Sheke Ayarsu a kan Gado
- Wani magajin gari a Brazil ya kama likita namiji da mace a wani ɗakin hutawa da aka kulle yayin da marasa lafiya ke jiran kulawa
- Carlinhos da Pedreira ya kai samame asibitin Jailton Messias de Albuquerque bayan korafe-korafen rashin kula da marasa lafiya
- Hukumomin lafiya sun yi Allah wadai da wulaƙanta likitocin a bainar jama'a, suna mai cewa ya kamata a bi hanyoyin doka wajen bincikarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Barreiros, Brazil - Wani magajin gari a ƙasar Brazil, Carlinhos da Pedreira, ya kama wasu likitoci biyu, namiji da mace, da ake zargin suna saduwa a lokacin aiki a wani asibiti.
Lamarin ya faru ne a daren ranar 4 ga watan Nuwambar 2026, lokacin da magajin garin ya kai ziyarar bazata asibitin ƙaramar hukumar Barreiros mai suna asibitin Jailton Messias de Albuquerque Municipal.

Kara karanta wannan
Nafiu Bala ya fito yana murna da rusa takarar Atiku da dukkan 'yan ADC a Najeriya

Source: Getty Images
Rahotanni sun nuna cewa magajin garin ya kai ziyarar ne bayan samun korafe-korafe daga al'umma kan yadda marasa lafiya ba sa samun kulawar da ta dace a asibitin, cewar TVC News.
A lokacin da ya isa sashen gaggawa, ya tarar da marasa lafiya sun cika wajen, amma likita guda ɗaya ne kawai daga cikin likitoci uku da ke bakin aiki yake kula da su.
Ya umurci a buɗe ɗakin da aka kulle
Bayan haka, magajin garin ya umurci a buɗe wani ɗakin hutawa da aka kulle, inda ya tarar da likita namiji da wata likita mace a ciki.
Ya fusata matuƙa, inda ya zarge su da yin abin da bai dace ba a lokacin aiki, musamman ganin yadda marasa lafiya ke jiran kulawa.
A cikin bidiyon da aka ɗauka lokacin faruwar lamarin, magajin garin ya ce:
"Abin da kuke yi ba abin karɓuwa ba ne. Sashen gaggawa ya cika da marasa lafiya, ku kuma kuna barci tare da gudanar da soyayya a nan."
Bayan faruwar lamarin, magajin garin ya nemi a cire likitocin daga bakin aiki tare da kiran jami'an 'yan sanda.

Source: UGC
An sauya masu kula da asibitin
Bayan faruwar lamarin, ƙaramar hukumar Barreiros da ke kasar Brazil ta sanar da kawo ƙarshen yarjejeniyar da ta kulla da ƙungiyar Associação Beneficente João Paulo II, wadda ke kula da gudanar da asibitin.
Hukumar ta ce za ta karɓi ragamar kula da asibitin kai tsaye har zuwa lokacin da za a kammala sabon tsarin neman wanda zai gudanar da shi.
Sai dai majalisar kula da harkokin likitanci ta yankin Pernambuco (Cremepe) ta yi Allah wadai da yadda aka wulaƙanta likitocin a bainar jama'a.
Majalisar ta jaddada cewa duk wani bincike ko matakin ladabtarwa kan likitocin ya kamata a gudanar da shi ta hanyoyin da doka ta tanada, tare da mutunta damar da suke da ita ta kare kansu.
Mace mafi tsayi ta rasu
A baya, an ji cewa Feliciana dos Santos, 'yar Brazil, wacce ta ajiye tarihi a matsayin mace mafi tsayi a duniya ta rigamu gidan gaskiya.

Kara karanta wannan
An kama mutum 3 kan zargin ƙona motar yan tawagar yakin neman zaben jam'iyyar APC
Santos wadda ta rasu tana da shekaru 77 a duniya ta rike kambun 'Sarauniyar Tsawo' a shekarun 1960 a Brazil.
A watan Mayun 2022, gidan tarihi na Museu de Gente Sergipana ya karrama Santos ta hanyar yin wani mutum-mutumi nata.
Asali: Legit.ng
