Gwamnatin Tarayya Ta Yi Bayani kan Shafukan da Mutum Zai Shiga domin Samun Tallafin N50,000
- Gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan shirin tallafin N50,000 yayin da aka fara yada wasu shafukan yanar gizo na damfara
- Ma’aikatar jin kai ta ce tallafin N50,000 na musamman ne ga talakawa da gidajen da ke cikin mawuyacin hali sakamakon tsadar rayuwa
- Ta ce ba a bukatar mutane su cike fom ko yin rajista, domin za a zabi wadanda suka cancanta daga rajistar marasa galihu ta kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Yayin da wasu sakonni ke yaduwa a kafafen sada zumunta, suna kira ga ‘yan Najeriya da su yi rajista domin samun tallafin N50,000 daga Gwamnatin Tarayya, Ma’aikatar Harkokin Jin Kai da Rage Talauci ta Tarayya ta yi karin haske.
Ma'aikatar ta bayani kan sahihancin shafukan da ake turawa ana bukatar mutane su shiga su cike domin samun tallafin N50,000.

Kara karanta wannan
Abin da Gwamnatin tarayya take so mutum ya yi idan aka tura masa saƙon tallafin N50,000

Source: Twitter
Shin shafukan da ake yadawa na gaske ne?
Daily Trust ta rahoto cewa a cikin wata sanarwa da Kingsley Onuoha, a madadin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, ya fitar, ya ce shafukan da ake yadawa na yan adambara ne.
Ya ce wadanda suka cancanci tallafin N50,000 su ne mutanen da ke cikin matsanancin talauci da mawuyacin hali.
Ya bayyana cewa za a zabo wadanda suka cancanta ne daga rajistar marasa galihu ta kasa (National Social Register) da bayanan shaidar dan kasa da aka tantance.
Onuoha ya ce shirin ya shafi dukkan shiyyoyin siyasa shida na Najeriya. Don haka, babu wani tsarin neman tallafin ta hanyar cike fom ko yin rajista, kuma babu wani mutum ko wakili da zai iya yin katsalandan wajen zaben wadanda za su amfana.
Ya kara da cewa duk wanda aka zaba zai samu tallafin N50,000 daga Gwamnatin Tarayya, kuma za a biya shi ba tare da cire ko sisi ba, domin tallafi ne ba bashi ba, don haka ba za a bukaci a mayar da kudin ba.

Kara karanta wannan
Hankali ya kwanta: An bayyana dalilin da ya sa wasu ba su samu saƙon tallafin N50,000 ba
Yadda za a gane wadanda aka zaba
Onuoha ya bayyana cewa hanya mafi inganci da mutum zai gane ko an zabe shi domin amfana da tallafin ita ce ta hanyar sakon SMS daga daya daga cikin kamfanonin hada-hadar kudi ta zamani da gwamnati ta amince da su.
Ya ce sakon zai kunshi umarnin yadda wanda aka zaba zai amince da karbar tallafin.

Source: Twitter
A cewarsa, bayan samun sakon SMS, wanda aka zaba ya kamata ya bi umarnin da kamfanin da aka ware domin biyan sa ya bayar, domin samun damar karbar kudin.
Ya bayyana cewa da zarar wanda aka zaba ya amince da karbar tallafin, za a tura masa N50,000 kai tsaye cikin asusun ajiyarsa na wayar hannu.
Karin bayani daga Gwamnatin Najeriya
Kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta bayyana abin da mutum ya kamata ya yi bayan an tura masa sakon cewa yana cikin wadanda za a ba tallafin N50,000.
Gwamnatin ta yi karin haske kan ko akwai ƙayyadadden lokacin da ’yan Najeriya za su amsa saƙon sanar da su cancantar samun tallafin NERSI.
Asali: Legit.ng