Sarki Sanusi II Ya Kuma Magana, Ya Ba Tinubu Shawarar da Za Ta Taimaki Gwamnatinsa
- Muhammadu Sanusi II, ya ce ya kamata a yaba wa Gwamnatin Bola Tinubu saboda inganta tattalin arzikin Najeriya
- Sarkin Kano ya ce hauhawar farashi ya ragu, tattalin arziki ya bunkasa, yayin da ajiyar kudin kasar waje ta karu
- Sai dai ya bukaci gwamnati ta inganta sadarwa da jama’a tare da sauraron koke-koken jama’a kan kuncin rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya ce Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya cancanci a yaba wa irin kokarinsa.
Sarkin Kano yana ganin cewa gwamnatin Bola Tinubu ta yi kokari wajen farfado da tattalin arziki, ta dawo da shi hayyacinsa.

Source: Twitter
Muhammadu Sanusi II a taron taron Oxford Global Think Tank
Muhammadu Sanusi II ya yi wannan magana ne a taron da Arunma Oteh ta shirya ranar Talata kamar yadda The Cable ta fada.
Arunma Oteh ta shirya taron Oxford Global Think Tank, inda Mai martaban ya yi magana game da halin tattalin arzikin Najeriya.
An ji cewa Khalifan darikar Tijjaniyan ya yi jawabi ne ta yanar gizo, bai samu zuwa taron da kafarsa ba.
Sarki Sanusi II ya yabi aikin Bola Tinubu
Sanusi II ya ce duk da bai cikin masoyan ‘yan siyasa, amma dole ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya ceto tattalin arzikin kasar nan.
“Ba na goyon bayan ’yan siyasa, amma ya kamata mu yaba wa gwamnatin Shugaba Tinubu bisa yadda ta ceto mu daga halin kuncin da muke ciki,”
- in ji shi.
Tsohon gwamnan babban bankin ya ce tattalin arzikin Najeriya ya karu da 4.48% a tsakiyar shekarnan, hakan ya nuna cigaba.
Idan aka kamanta da karfin tattalin kasar lokacin Muhammadu Buhari, Sarkin Kano yana ganin gwamnatin Tinubu ta yi abin a yaba.
Sai dai duk da haka, bai kai irin cigaban da aka samu lokacin da Ummaru Yar’adu da Goodluck Jonathan suke kan mulki ba.
Ya kuma yi murna da tsadar kaya ya sauka daga kusan 30% zuwa 14.%, kuma masana suna hasashen zai sauka zuwa 12.5%.
Masanin tattalin ya kuma ce jimillar karfin tattalin arzikin Najeriya (GD) ya karu da 47% a shekar bana.
Sarki ya ce idan aka cigaba da tafiya a haka, GDP zai kai yadda yake a shekarar 2005 lokacin Olusegun Obasanjo yana mulki.
Duk da abin da yake cikin asusun kudin kasar wajen Najeriya ya kai $55bn a yau, Sanusi II yana ganin akwai sauran aiki.
Tsohon gwamnan CBN ya alakanta kudin da Najeriya ta ke samu da rikicin da ake yi da Iran wanda ya jawo tsadar danyen mai.
Shawarar da Sarkin Kano ya ba Gwamnatin Tinubu
Daily Trust ta rahoto shi yana ba shugabanni shawara cewa sukar gwamnati bai nufin kiyayya ko ana kokarin taba shugaban kasa.
An samu nasarori, amma tsohon gwamnan bankin na CBN ya ce daga an soki gwamnati, sai ta dauka cewa ana faman fada ne da ita.
“Wannan gwamnati ba ta iya bayyana manufofinta yadda ya kamata. Tana ɗdukar duk wata shawara ko gudummawar da ba ta so a matsayin suka, sannan ba ta da kwararrun masu magana da yawunta.”

Kara karanta wannan
Tsohon sanata kirista ya kalubalanci Shugaba Tinubu ya zo su yi gasar karatun Kur'ani
“Ba duk lokacin da mutane ke magana kan talauci ko matsalolin rayuwa ba ne suke adawa da gwamnati ko caccakar shugaban kasa.
Ba haka ya kamata a rika mayar da martani ga matsin tattalin arziki ba,”
- Muhammadu Sanusi

Source: Twitter
Gwamna ya zargi Muhammadu Buhari da rusa tattali
Ana da labari Gwamna Caleb Mutfwang ya ce gwamnatin da ta wuce ta durkusa tattalin arzikin kafin a yi canjin mulki a 2023.
Gwamnan Filato ya zargi marigayi Muhammadu Buhari da yamutsa tattalin arziki gabanin shigan mai girma Bola Tinubu ofis.
Caleb Muftwang yake cewa Buhari sun saida danyen man Najeriya tun kain a hako shi da suka rasa yadda kasar za ta samu kudi.
Asali: Legit.ng

