Tsohon Sanata Kirista Ya Kalubalanci Shugaba Tinubu Ya Zo Su Yi Gasar Karatun Alku'ani
- Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya kalubalanci Shugaba Bola Tinubu da ya zo su yi gasar karanta ayoyin Alkur’ani
- Melaye ya bayyana kalubalensa ne a wani sako da ya wallafa yayin da ake yada labari cewa Tinubu ya samu damar shiga dakin Ka'aba
- Tinubu ya ce ya roki Allah hikima da juriyar ci gaba da yi wa 'yan Najeriya hidima yayin ziyararsa ta ibada a kasar Saudiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kogi, Nigeria - Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya kalubalanci Shugaban kasa Bola Tinubu zuwa gasar karanta ayoyin Alkur’ani bayan ziyarar ibadar da shugaban ya kai kasar Saudiyya.
Sanata Melaye, wanda kirista ne ya bukaci Tinubu ya shirya su yi gasar karanta Alkur'ani idan ya dawo daga Najeriya daga Umrah.

Source: Twitter
Melaye ya kalubalanci Tinubu
Melaye ya yi wannan kalubale ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin, inda ya ce a shirye yake ya fafata da Tinubu wajen karanta ayoyin Alkur’ani idan ya dawo.
Ya rubuta cewa:
“Yanzu da Alhaji Bola Tinubu yake Umrah, da zarar ya dawo, ina kalubalantarsa zuwa gasar karanta ayoyin Alkur’ani tsakanina da shi. Babu wanda zai iya yi wa Allah izgil.
Dalilin kalubalen Dino Melaye
Kalubalen ya zo ne bayan ziyarar ibadar da Tinubu ya kai Saudiyya, inda ya gudanar da Umrah, tare da samun damar shiga dakin Ka’aba mai alfarma tare da wasu mambobin tawagarsa.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Litinin, Tinubu ya ce ya roki Allah ya ba shi hikima da juriyar ci gaba da yi wa 'yan Najeriya hidima.
Ya kuma jaddada kudurinsa na ci gaba da kokarin bunkasa kasa da wadata al'ummarta.
Abin da Tinubu ya roka a Ka'aba
Sanarwar ta ambato Tinubu yana cewa:
“To, na roki Allah ya ba ni hikima da juriyar ci gaba da yi wa al’umma hidima. Na san an amsa addu’ata. Kafin zaben 2023, na yi irin wannan abu. Na roki Allah ya karbi Umrah dina a lokacin, kuma Ya karba. Na yi alkawarin zan dawo domin gode Masa.”
Tinubu ya kuma nuna godiyarsa ga Sarkin Saudiyya, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, bisa ba shi damar yin sallah a cikin dakin Ka’aba mai alfarma, wadda ba kasafai ake samu ba.

Source: Facebook
Yayin da ake tsokaci kan wannan lamari, Dino Melaye ya bukaci Tinubu da ya zo su yi gasar karatun Alkur'ani idan ya dawo gida Najeriya.
Tinubu ya mika lamurransa ga Allah
A wani labarin, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana imaminsa cewa Allah ne kadai ke bayar da mulki kuma yake karɓe shi a lokacin da ya so.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa Allah zai iya karɓe mulkin daga hannunsa ya ba wani idan bai yi amfani da shi bisa umarninSa ba.
Ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi jim kadan bayan ya samu damar shiga dakin Ka'aba a kasar Saudiyya.
Asali: Legit.ng


