Maganar da Abdussamad Rabiu Ya Yi bayan Bude Masu Ka’aba tare da Tinubu
- Abdul Samad Rabiu, ya bayyana shiga Ka’aba tare da Bola Tinubu a matsayin babbar ni’ima a rayuwarsa
- Shugaban BUA ya ce ya yi addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Najeriya da ya shiga dakin
- Alhaji Abdul Samad Rabiu ya gode wa Allah bisa wannan dama ta musamman da ya samu a rayuwar shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Saudi Arabia - Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya ji dadin shiga Ka’aba da ya yi a makon jiya.
Attajirin ya bayyana shiga cikin dakin mai alfarma tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin wata babbar ni’ima.

Source: Facebook
Abdul Samad Rabiu ya yi magana bayan shiga ka'aba
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, hamshaƙin attajirin ya bayyana farin cikinsa da godiyarsa ga Allah SWT.
Ya yi farin ciki sosai bisa samun damar shiga wannan wuri mafi tsarki a Musulunci tare da shugaban Najeriya ranar Lahadi.
‘Dan kasuwan ya ce ba kasafai mutum ke samun dama irin wannan a rayuwarsa ba.
Abdul Samad Rabiu ya ce:
“Wasu lokuta a rayuwa sun fi ƙarfin kalmomi wajen bayyana su. Lokuta ne da suke taɓa zuciya kuma su zauna a cikinta har abada.
“Alhamdulillah, a yau na ji ƙanƙan da kai tare da godiya ga Allah bisa kasancewa cikin waɗanda suka samu wannan babbar dama ta shiga cikin Ka’aba mai alfarma tare da mai girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu.”
Addu'ar da Abdul Samad ya yi a ka'aba
Attajirin ya bayyana cewa wannan ziyara ta kasance wata babbar dama da ya yi amfani da ita wajen yin addu’o’i ga Najeriya.
An ji cewa ‘dan kasuwar ya roki zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban tattalin arziki a Najeriya.
Ya ƙara da cewa:
“A wannan wuri mafi tsarki, addu’o’ina ba su tsaya kan kaina da iyalina kawai ba, sun haɗa da ƙasarmu baki ɗaya.
Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya karɓi addu’o’inmu, Ya albarkaci ƙasarmu da zaman lafiya mai ɗorewa, haɗin kai da wadata.”
Ya ce wannan ni’ima ce da mutum zai iya samu sau ɗaya a rayuwarsa, kuma wata dama ce da ba za a iya auna darajarta ba.
Babban mai kudin naNajeriya ya bayyana cewa wannan dama mai tsarki ta ƙara masa godiya ga Allah, tunani da ƙarfafa imaninsa.
Tsarin buɗe ƙofar Ka’aba a Saudi
Shiga cikin Ka’aba na daga cikin abubuwan da ba kasafai ake ba wa mutane dama ba, domin hukumomi suna tsaurar matakai.
Premium Times ta ce dokar Saudiyya ta tanadi cewa ba za a buɗe ƙofar Ka’aba ba sai da umarni na musamman daga Sarki.
Sai da yardar Sarki mai kula da Masallatai Masu Alfarma Biyu, ko Yarima Mai Jiran Gado, Mohammed bin Salman ake iya shiga.

Kara karanta wannan
PRP ta yi kaca kaca da shirin Tinubu, ta taɓo batun kisan Sheikh Yahaya Masussuka
Buɗe Ka’aba domin shugaban ƙasa a Musulmi da ya kai ziyara Saudi na nuna girmamawa ta musamman daga masarautar.
Liyafar Tinubu da gwamnoni da su Abdul Samad
An ji labari Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shirya wata liyafar cin abinci ta musamman a birnin Makkah inda ya tarbi wasu manyan hadimansa da gwamnoni.
Wadanda suka halarci taron sun hada da gwamnonin jihohi irin su Uba Sani da Babagana Umara Zulum, tare da 'yan kasuwa kamar Abdussamad Rabiu.
Shugaban na Najeriya ya yi addu'ar Allah ya sa bambancin kasar ya zama abin karfafa hadin kai da ci gaba maimakon rabuwar kawuna babu gaira babu dalili.
Asali: Legit.ng

