Gwamnatin Tinubu za Ta Kawo Dokar Tattalin Arziki da za Ta Yi Aiki ko da Ya Sauka
- Gwamnatin Tarayya na duba yiwuwar samar da doka da za ta hana gwamnatocin da za su biyo baya soke manyan sauye-sauyen tattalin arzikin Najeriya
- Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya ce ana neman ra’ayin ’yan Najeriya kan tsarin manufofin tattalin arziki da za a iya mayar da su doka domin tabbatar da dorewarsu
- Ya bayyana cewa za a ci gaba da tattaunawa kan tsarin har zuwa ranar 27 ga Nuwamba, 2026, kafin miƙa shi ga hukumomin gwamnati domin amincewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya na nazarin yiwuwar samar da doka da za ta kare sauye-sauyen tattalin arzikin Najeriya daga sokewa ko sauya su daga gwamnatocin da za su biyo baya.
Ministan Kuɗi kuma mai kula da tattalin arzikin ƙasa, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin taron koli na tattalin arzikin Najeriya karo na 32 da aka gudanar a Abuja.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa taken taron shi ne “Ci gaban da ke Amfanar Jama’a: Samar da Ayyukan Yi, Haɓaka Ƙwarewa da Tabbatar da Wadata ga Kowa.”
Matakan da gwamnati za ta dauka
Oyedele ya ce gwamnati na neman haɗin kan ’yan Najeriya wajen samar da tsarin manufofin tattalin arziki na ƙasa da za a iya mayar da shi doka.
Ya bayyana cewa tsarin zai ƙunshi ƙa’idojin da za su jagoranci yanke shawarar gwamnati a nan gaba, musamman kan haraji, kuɗi, tallafi, zuba jari da bunƙasa masana’antu.
Ministan ya ce ana buƙatar tabbatar da cewa manufofin ba za su tsaya ga sanarwar gwamnati kawai ba, sai dai su samu gindin zama a hukumomi da dokokin ƙasa.
A cewarsa:
“Yanzu muna buƙatar tabbatar da dorewar tsarin ta hanyar hukumomi, doka da kuma tsarin manufofi, domin ya dawwama.”
Ya ce manufar ita ce hana gwamnatocin da za su zo nan gaba yin watsi da sauye-sauyen tattalin arziki saboda buƙatun siyasa na ɗan lokaci.
Magana kan maido tallafin mai
Premium Times ta wallafa cewa ministan ya yi magana kan yiwuwar wata gwamnati ta dawo da tallafin man fetur, yana mai cewa ya kamata a yi watsi da irin wannan tunani a ƙarƙashin tsarin da ake son samarwa.
Ya ce tsarin zai ƙunshi tambayoyi da za su taimaka wajen tantance ko ya kamata a mayar da wasu manufofin tattalin arziki doka da kuma yadda za a ƙarfafa hukumomin da ke aiwatar da su.
Oyedele ya bayyana cewa gwamnati na son samar da tsarin da zai tilasta wa jami’an gwamnati da waɗanda aka naɗa kan muƙaman siyasa fahimtar ƙa’idojin tattalin arzikin da aka amince da su tare da bin su.

Source: Facebook
Ya ce ana iya haɗa tsarin cikin tantance mutanen da za a naɗa muƙaman gwamnati, ta yadda za a tabbatar sun fahimci manufofin tattalin arzikin ƙasar.
Haka kuma, ana iya haɗa kwafin tsarin da takardun naɗin muƙamai domin ya zama jagora wajen yanke shawara kan manufofin tattalin arziki.
IPOB na adawa da APC
A wani labarin, kun ji cewa ƙungiyar IPOB ta sanar da kauracewa jam’iyyar APC tana mai danganta matakin da abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnati wajen tabbatar da sauraron ɗaukaka ƙarar Nnamdi Kanu.
Ƙungiyar ta ce matakin nata ya biyo bayan rashin sanya ƙarar ɗaukaka hukuncin da aka yanke wa Kanu a ranar 20 ga Nuwamba, 2025, cikin jerin shari’o’in da za a saurara a Kotun Ɗaukaka Ƙara.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta, Emma Powerful, ya fitar a ranar Litinin, ƙungiyar ta ce ba za ta shiga harkokin siyasa, tallafa wa APC ko taimaka mata ba.
Asali: Legit.ng


