Abubawan da ke jawo hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya

Abubawan da ke jawo hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya

- A yau ne Ofishin Kididdiga ya sanar da hauhawar farashin tattalin arziki a Najeriya

- Lamarin ya jawo kara tashin kayayyaki musamman na abinci a fadin kasar baki daya

- Masanin tattalin arzik ya bayyana dalilin da ke jawo har farashin kayayyakin ke tashi

A yau Alhamis 15 ga watan Afrilu ne Ofishin Kididdiga na kasa ya fidda rahoton da ke nuni da karuwar wani kaso a hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya.

Rahoton ya bayyana tashin farashin daga 17.33% zuwa 18.17% a tsakanin watannin Fabrairu da Maris na wannan shekarar ta 2021.

Domin amsa tambayoyin da 'yan Najeriya kan iya yi game da dalilan da ke jawo hauhawar farashin kayayyaki, wakilinmu a Legit.ng Hausa ya tattauna da wani masanin tattalin arziki daga kamfanin One 17 Capital Limited, Ismail Rufai.

KU KARANTA: Rashin kwarewar Buhari a mulki ne ya sa Twitter ta kai hedkwatarta Ghana, PDP

Abubawan da ke jawo hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya
Abubawan da ke jawo hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya Hoto: financialexpress.com
Asali: UGC

Masanin ya alakanta hauhawar farashin da abubuwa guda biyu; karuwar yawan jama'a da kuma bukatun kayayyaki da ake dashi wanda samar da kayayyakin ba zai wadatar ba.

Da aka tambayeshi dangane da dalilin da ke jawo hauhawar farashi, Rufai ya amsa da cewa:

"Babban dalilin da yasa muke yawan samun hauhawar farashi shine lokacin da muke da bukata sama da samar da kayayyaki da aiyuka.

"Don haka, a halin yanzu a Najeriya, muna cikin halin da ake ciki ne saboda yawan jama'a, yawan bukatun kayayyaki da ayyuka yana karuwa yayin da wadatar da take daidai ba ta karuwa kamar yadda bukatar ke karuwa."

Ya kuma yi tsokaci kan mafita dangane da matsalar ta hauhawar farashin, ya ce, "ina tsammanin ainihin mafita shine, idan muna da daidaito a cikin karfin samar da tattalin arziki"

Ya kuma ja hankalin gwamnati wajen inganta tsaro da ba da gudunmawar ta ga kamfanoni don samar da ainihin abinda ake bukata.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun dakile yunkurin balle gidan yarin Ubiaja na jihar Edo

A wani labarin, Kididdigar farashin mabukaci, wanda ke auna kimar karuwar farashin kayayyaki da aiyuka, ya karu zuwa 18.17% a watan Maris daga 17.33% a watan Fabrairu.

Wannan ya fito ne a cikin rahoton farashi na watan Maris na 2021/rahoton hauhawar farashin kaya wanda Ofishin Kididdiga na Kasa ya fitar a ranar Alhamis.

Hawan farashin abinci ya kuma karu da 1.16% bisa dari 100% a shekara daga 21.79% a watan Fabrairu zuwa 22.95% a watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel