Gwamnan APC Ya Fallasa Danyen Aikin da Buhari Ya Yi da Ya bar Tinubu da Wahala

Gwamnan APC Ya Fallasa Danyen Aikin da Buhari Ya Yi da Ya bar Tinubu da Wahala

  • Caleb Mutfwang ya yi bayanin halin da Muhammadu Buhari ya damka wa Bola Tinubu mulki a shekarar 2023
  • Ya ce kafin wancan gwamnatin ta bar mulki, sai da ta saida man da ba a kai ga hako shi daga cikin kasa ba
  • Gwamnan Filato ya kare manufofin shugaba Tinubu tare da yin bayanin nasarorin da aka samu a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Plateau - Caleb Mutfwang, ya zargi gwamnatin Muhammadu Buhari da sayar da ɗanyen mai tun kafin a haƙo shi daga ƙasa.

Gwamnan Jihar Filato ya ce har yanzu gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu tana biyan bashin da aka ci sakamakon hakan.

Gwamna Caleb
Gwamnan Filato tare da Shugaban kasa Bola Tinubu a Abuja Hoto: Caleb Muftwang
Source: Facebook

An bude yakin zaben Bola Tinubu a Plateau

Caleb Mutfwang ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a cewar Vanguard.

An bude kamfen jam’iyyar APC ne a yau gidan gwamnatin jihar da ke Rayfield, Jos a jihar Filato.

Kara karanta wannan

Kebbi: Gwamnati ta yi maganar ‘rusa’ ginin tsohon ministan Buhari, Abubakar Malami

Mai girma Gwamnan ya jero nasarorin da aka samu, yana mai kwarin gwiwar cewa APC za ta lashe zaɓen 2027 a Filato.

Gwamna ya zargi Muhammadu Buhari da rusa tattali

Gwamnan ya ɗora alhakin matsalolin tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta gada a shekarar 2023 kan gwamnatin da ta gabata.

Mai girma Muftwang ya ce ya kamata a ba gwamnatin yanzu lokaci domin sauye-sauyen da take yi su fara haifar da ‘da mai ido.

Ya ce:

“Ɗaya daga cikin matsalolin gwamnatin Buhari shi ne ta kai wani mataki da ba ta san abin da za ta yi ba, don haka ta sayar da ɗanyen man da za a haƙo nan gaba.
“An riga an sayar da man da har yanzu ba a haƙo daga ƙasa ba. Yanzu kuma muna biyan bashin wannan ciniki. Saboda haka, ba za mu yi tsammanin komai zai canza cikin dare ɗaya ba.”

Damfarar da ke cikin tallafin man fetur

Gwamnan Filato ya kuma bayyana tsarin tallafin man fetur na gwamnatin da ta gabata a matsayin wata babbar damfara a ƙasa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kawar da shakkun 'yan Najeriya, ya fadi dalilinsa na runtumo basussuka

Ya ce ‘yan kasuwa suna kawo takardun bogi, su nemi kuɗi da sunan tallafin mai. da suka saida da araha.

‘Dan siyasar ya ce bai dace a ci gaba da karɓar bashi ana ba ɓarayi kuɗi ba, don haka ya ce dole ne a dakatar da wannan tsari.

Punch ta ji shi yana cewa a baya, Gwamnatin tarayya ta riƙa karɓo aron kuɗin domin biyan tallafin da aka gabatar da takardun bogi.

"Lokacin da Shugaban Ƙasa ya karɓi mulki, akwai wata babbar damfara da ake yi a ƙasa da sunan tallafin man fetur.
"Na kira shi damfara ne saboda muna karɓar bashi domin biyan mutanen da suke kawo takardun ƙarya. Ba su samar da wata dukiya ba."

- Gwamna Caleb Muftwang

Wasu nasarorin da Bola Tinubu ya samu

Ko da yake da tsada, Mutfwang ya ce cire tallafin fetur ya taimaka wajen inganta samun mai akasin yadda aka saba layi a da.

Gwamnan ya kuma kare manufofin tattalin arzikin Tinubu, inda ya yi iƙirarin cewa asusun ajiyar kuɗin waje ya haura $50bn.

Kara karanta wannan

An tura fitacciyar fim kurkuku kan zargin fitar da hoton tsiraici

Ya ce lokacin da Tinubu ya karɓi mulki a 2023, Najeriya na daf da durƙushewa ta fuskar tattalin arziki, biyan bashi ya gagara.

Caleb Muftwang
Gwamnonin APC wajen yakin zabe a Kaduna Hoto: Caleb Muftwang
Source: Facebook

Shugaba Tinubu ya kare cire tallafin fetur

Ana da labari Bola Tinubu ya sake kare cire tallafin man fetur, yana mai cewa hakan ya kawo karshen rashin gaskiya a Najeriya.

Shugaban kasar ya zargi jam’iyyun adawa da jawo yunwa da talauci a Najeriya yayin kaddamar da yakin neman zabensa a Kaduna.

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya jaddada goyon bayan da Tinubu ya dade yana ba wa 'yan siyasar Arewa a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng