Yayin da Rikicin Mashigar Hormuz ke Kara Tsananta, Farashin Mai Ya Tashi a Najeriya
- Farashin fetur ya yi tashin gwauron zabi a wasu gidajen mai a Abuja, yayin da rikicin mashigar Hormuz ke kara tsananta
- Matatar Dangote ta kara farashin man fetur daga N1,265 zuwa N1,350 kan lita, lamarin da ya jawo karin farashi a Abuja
- Masana sun yi gargadin cewa karin farashin fetur zai kara tsadar sufuri, abinci da kayayyaki, tare da jefa ’yan Najeriya cikin karin wahala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gidajen mai da dama a Babban Birnin Tarayya Abuja sun ci gaba da kara farashin man fetur, wanda aka fi sani da PMS.
Sabon karin farashin ya biyo bayan karin N85 da Matatar Dangote ta yi kan farashin man fetur daga N1,265 zuwa N1,350 kan lita, yayin da farashin danyen mai a duniya ke karuwa.

Kara karanta wannan
Ana cikin wahala a ƙasa, Atiku, Tinubu sun kwashi miliyoyin dala sun kashe a Amurka

Source: Getty Images
Farashin mai ya tashi a Abuja
Wannan karin ya kai kashi 6.7 cikin 100, inda farashin sayar da man fetur daga matatar ya haura farashin sauke fetur da ake kiyasta N1,311 kan lita, cewar Daily Trust.
Danyen Brent, wanda ake amfani da shi wajen auna farashin man Najeriya, ya kai kusan dala 107.92 kan ganga, sannan ya kara zuwa dala 108.21.
Karin farashin ya kara matsin lamba kan masu gudanar da harkokin man fetur, tare da haddasa karin farashi a gidajen mai daban-daban a Abuja.
Hakan na nufin masu ababen hawa za su iya fuskantar karin kudin fetur a gidajen mai a makonni masu zuwa, lamarin da zai kara tsadar sufuri da nauyin rayuwa ga iyalai.
Wani bincike a Abuja ranar Lahadi ya nuna cewa wasu gidajen mai sun fara kara farashin fetur, inda masu motoci ke biyan karin kudi.
An gano cewa gidajen mai na MRS sun kara farashin fetur daga N1,350 zuwa N1,395 kan lita, yayin da NIPCO ta kara shi daga N1,350 zuwa N1,430, haka kuma, gidajen mai na Mobil sun kara farashin daga N1,350 zuwa N1,400 kan lita.
Wata ma’aikaciyar gidan mai na MRS, wadda ta bukaci a boye sunanta, ta ce ana iya sake kara farashin fetur daga gobe.
Ya ce:
"A yanzu muna sayar da tsohon man da ke hannunmu kan N1,395 kan lita, amma daga gobe, da zarar sabon kaya ya iso, farashin zai fi haka.”

Source: Facebook
Abin da masana ke cewa
Dr Aliyu Ilias, wani masanin tattalin arziki kuma kwararre kan ci gaba, ya ce sabon karin farashin fetur na iya kara hauhawar farashin kayayyaki da tsananta matsin tattalin arziki ga ’yan Najeriya.
Ilias ya ce karin farashin fetur zai iya haifar da karin kudin sufuri da na samar da kayayyaki, musamman abinci da sauran muhimman abubuwa.
Mista Owei Lakemfa, tsohon Sakataren Kungiyar Hadin Kan Kungiyoyin Kwadago na Afirka, OATUU, ya ce dole Najeriya ta kare masu amfani daga illar sauyin farashin danyen mai a duniya.
Lakemfa ya ce kasar na bukatar karfafa tsare-tsaren tattalin arziki da tsarin kula da harkokin man fetur domin cimma hakan.
A cewarsa, kasa irin Najeriya wadda ke samar da danyen mai kuma ke da dimbin jama’a, ya kamata ta dauki matakan kare al’ummarta daga karin farashin man fetur kwatsam.
Sakataren Yada Labarai na Kungiyar ’Yan Kasuwar Man Fetur ta Najeriya, IPMAN, Chinedu Ukadike, ya ce ’yan kasuwar sun sake duba farashin fetur bayan jerin karin farashin da Matatar Dangote ta yi.
Ukadike ya ce sauye-sauyen farashin da ake samu akai-akai na haifar da rashin tabbas ga ’yan kasuwa da masu amfani, saboda kudin da ake bukata wajen maye gurbin man da aka sayar na iya sauyawa.
Dangote ya kara farashin man fetur
Mun ba ku labarin cewa Matatar Dangote ta ƙara farashin man fetur da take sayarwa a farfajiyar matatar da Na85 kan kowace lita, daga N1,265 zuwa N1,350.
Karin ya zo ne yayin da farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya da kuɗin maye gurbin man fetur ke ci gaba da tashi.
Sabon farashin ya haura matsakaicin kuɗin saukar da man fetur na yanzu da aka sanya a N1,311 kan lita, abin da ke ƙara matsin lamba a harkar mai.
Asali: Legit.ng

