Sheikh Gumi Ya Bayyana Abin da Suka Tattauna da Ƴan Bindiga, Akwai Zarge Zarge

Sheikh Gumi Ya Bayyana Abin da Suka Tattauna da Ƴan Bindiga, Akwai Zarge Zarge

  • Sheikh Ahmad Gumi ya ce wasu ’yan bindiga sun bayyana masa cewa ba sa farin cikin kashe-kashen, amma suna ganin an tilasta musu ci gaba da kai hare-hare
  • Malamin ya ce ’yan bindigar na kallon rikicin a matsayin ramuwar gayya tsakanin su da al’ummomin da ke kai musu hare-hare
  • Gumi ya bayyana cewa tsoron kada a kashe su idan sun ajiye makamai na daga cikin dalilan da ke hana su mika wuya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa wasu ’yan bindiga da ya tattauna da su sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda ake ci gaba da zubar da jini a Najeriya.

Gumi ya ce ’yan bindigar sun bayyana cewa suna jin dole ne su ci gaba da kai hare-hare saboda kashe-kashen da ake yi a cikin al’ummominsu.

Kara karanta wannan

Yadda aka ceto malaman da aka sace za su tafi yi wa Tinubu addu'a a Zamfara

Sheikh Gumi ya yi magana kan hare-haren yan bindiga
Babban malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi. Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi.
Source: Facebook

Malamin ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin PAPShow, wadda aka wallafa a ranar 29 ga Oktoba, da Punch ta samu wasu sassan hirar.

Ya kara da cewa wasu daga cikinsu suna ganin za a iya kashe su idan suka ajiye makamai ko suka daina ayyukan ta’addanci.

Gumi ya bayyana korafin ’yan bindiga

A cewar Gumi, daya daga cikin ’yan bindigar da ya tattauna da shi ya amince cewa kashe-kashen da ake yi sun yi yawa, duk da cewa suna ganin an tilasta musu ci gaba da tashin hankalin.

Ya ce:

“Daya daga cikin ’yan bindigar yana gaya mana cewa zubar da jinin ya yi yawa, su ma ba sa farin ciki. Amma suna cewa an tilasta musu yin hakan.”

Da yake bayanin korafe-korafen ’yan bindigar, malamin ya ce sun zargi jami’an soji da kashe mata da yara a yankunansu yayin wasu hare-haren da aka ce an kai domin dakile satar shanu.

Kara karanta wannan

Bincike ya gano shan fitsari da sauran azabar da mutanen da suka mutu hannun NSCDC suka sha

Ya ce ya tambayi dalilin da ya sa ake kashe mata da yara a yayin irin wadannan samame.

Gumi ya ce ’yan bindigar sun yi tambayoyi kan dalilin da ya sa ake kashe matansu da yaransu, tare da zargin ’yan sa-kai da kama su da kashe su.

A cewarsa, ’yan bindigar suna kallon lamarin a matsayin wani mummunan zagayen ramuwar gayya, inda bangarorin biyu ke kai hare-hare kan juna.

Sheikh Gumi ya ba da shawara game da hare-haren yan bindiga
Malamin Musulunci daga jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi. Hoto: Dr. Ahmad Mahmud Gumi.
Source: Twitter

Gumi ya bukaci a yi sulhu da ’yan bindiga

Malamin ya bayyana cewa ci gaba da kashe-kashen ya sa tattaunawa ta zama dole domin kawo karshen matsalar tsaro.

Ya ce akwai bukatar shugabannin addinai su taka rawar gani wajen karfafa bangarorin da ke rikici da juna su zauna kan teburin sulhu.

Gumi ya ce:

“Saboda haka, a matsayinmu na malaman addini, aikinmu shi ne duba yadda za mu dakatar da wannan matsala. Mu dakatar da zubar da jini, mu zauna mu tattauna.”

Yayin da mai gabatar da shirin ya tambaye shi dalilin da ya sa ’yan bindigar ba za su iya dakatar da ayyukansu ba, Gumi ya ce suna tsoron za a kashe su idan suka mika wuya.

Kara karanta wannan

Abin da aka gani a jikin gawar Sheikh Yahaya Masussuka bayan kai ta asibiti a Katsina

Ya bayyana cewa:

“Saboda suna tunanin za a kashe su. Don haka, muna bukatar mu tabbatar musu da cewa ba za a kashe su ba domin su samu kwarin gwiwar ajiye makamai.”

Gumi ya yi zargin kasashen ketare

Malamin ya kuma yi ikirarin cewa wasu hukumomin leken asiri na kasashen ketare na iya kasancewa da hannu wajen samar da makamai ga kungiyoyin masu dauke da makamai.

Sai dai bai gabatar da wata hujja da za ta tabbatar da wannan zargi ba, da aka tambaye shi ko kasashen ketare na iya bai wa ’yan bindiga da ’yan ta’adda makamai a Najeriya, Gumi ya ce hakan abu ne mai yiwuwa.

Ya kara da cewa duk wata kasa da ke da muradin shiga harkokin Najeriya na iya kasancewa tana da hannu a irin wadannan ayyuka, amma bai kawo hujjojin da ke tabbatar da ikirarinsa ba.

Masussuka: Gumi ya magantu kan kisan malamin

An ji cewa Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana kisan Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka a matsayin babban kuskure da ka iya jawo fitina a cikin al’umma.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda a Borno, sun kashe kusan 50

Malamin ya yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar maƙiyan Musulunci su yi amfani da lamarin wajen haifar da ruɗani.

Gumi ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, su bar hukuma ta ɗauki matakin da ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.