Yadda aka Ceto Malaman da aka Sace za Su Tafi Yi wa Tinubu Addu'a a Zamfara
- Rundunar ’yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da ceto limaman Musulunci uku daga cikin shida da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a ranar 12 ga Satumba
- Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Muhammad Bello, ya ce an ceto limaman ne ta hanyar hadin gwiwar jami’an tsaro daga hukumomi daban-daban, ciki har da DSS
- Ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da samame domin gano sauran limaman uku da ke hannun masu garkuwa da mutane tare da kubutar da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jiihar Zamfara - Rundunar ’yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da ceto malaman Musulunci uku daga cikin shida da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a watan Satumba.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Muhammad Bello, ne ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a yayin wata hira da wasu ’yan jarida a Gusau.

Source: Facebook
Vanguard ta rahoto ya ce an samu nasarar kubutar da limaman ne sakamakon hadin gwiwar ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA), hukumar DSS da jami’an rundunar ’yan sanda.
Yadda aka ceto malamai a Zamfara
Bello ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi amfani da bayanan sirri da hadin gwiwa tsakanin hukumomi wajen gudanar da aikin ceto limaman.
Tribune ta rahoto ya ce jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da samame a yankunan da ake zargin ’yan bindigar suke, domin gano sauran limaman uku da ke tsare a hannun masu garkuwa da mutane.
Kwamishinan ya kara da cewa bayanan sirri da al’ummar yankunan ke bayarwa a kan lokaci na taimaka wa jami’an tsaro wajen bin diddigin masu laifin.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), wani babban jami’in tsaro da ya shiga aikin ceton ya tabbatar da cewa an kubutar da limaman uku ba tare da sun samu rauni ba.

Source: Original
Yaushe aka sace malaman?
Rahotanni sun nuna cewa an yi garkuwa da limaman ne a ranar 12 ga Satumba, lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Talata Mafara domin halartar wani taron addu’a na musamman ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Masu garkuwar sun tare motarsu ne da misalin karfe 11:30 na safe a hanyar Dakko-Damri, kusa da dajin Sububu da ke karamar hukumar Bakura.
Daga cikin sunayen limaman da aka ambata akwai Imam Yahuza, Magawata Abdullahi, Malam Shehu Dakko, Imam Bala Fagon da Na’ibi Tasi’u.
Rahoton ya ce masu garkuwar sun bukaci a biya su kudin fansa har Naira miliyan 30 domin sakin limaman.
Wani jami’in tsaro ya tabbatar da cewa limaman uku da aka ceto suna cikin koshin lafiya, bayan an duba lafiyarsu tare da gudanar da binciken da ya dace domin tantance halin da suke ciki.
An kai wa 'yan ADC hari
A wani labarin, kun ji cewa dan takarar gwamnan jihar Sokoto na jam’iyyar ADC, Hon. Manir Muhammad Dan’iya, ya nuna damuwa kan barazanar da ya ce an yi wa rayuwarsa.
Dan’iya ya yi zargin cewa jami’an rundunar Sokoto Marshal da hukumar Community Guard Corps ta jihar ne suka kai wa ayarin motocinsa hari a kusa da filin jirgin saman Sokoto.
A cikin sanarwar da hadiminsa kan harkokin yada labarai, Aminu Abdullahi, ya fitar, dan takarar ya ce jami’an sun tare ayarinsa tare da hana shi wucewa.
Asali: Legit.ng


