Bincike Ya Gano Shan Fitsari da Sauran Azabar da Mutanen da Suka Mutu hannun NSCDC Suka Sha
- Rahoto ya gano cewa mutane 33, ciki har da yara 14, sun mutu a hannun hukumar NSCDC a jihar Neja
- Sun mutu ne sakamakon an tsare su cikin cunkoso, kuma sun yi fama da rashin isasshen iska da ruwa
- Wasu cikin wadanda aka kama sun sha fitsari da zufa saboda ƙishirwa, amma jami’an NSDC suka ki tanka su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Niger - Rahoton kwamitin bincike ya bayyana halin da mutanen aka tsare a ofishin NSCDC a jihar Neja suka shiga.
A hannun jami’an hukumar NSCDC ne wasu daga cikin wadannan bayin Allah suka rasu, hakan ya jawo ake yin bincike.

Source: Twitter
NSCDC ta ki daukar shawarar malaman lafiya
Premium Times ta kadaita da wani rahoto da ya ce mutanen da aka tsare sun sha fitsari da gumi saboda rashin ruwan sha
Kwamitin ya kuma gano cewa jami’an hukumar sun yi biris da gargaɗin da aka yi musu kan cunkoson wadanda suka tsare.
An yi masu bayanin haɗarin da ke tattare da rashin iska a ɗakin da aka tsare mutanen da fiye da 30 daga cikinsu suka mutu.
Kwamitin bincike ya fito da bayanai
Kwamitin bincike mai zaman kansa da ma’aikatar harkokin cikin gida ta tarayya ta kafa ya fito da wadannan bayanai.
Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamiti na musamman domin binciken mutuwar mutane da dama.
Rahoton da aka samu ya ce ɗakin da jami’an NSCDC ta tsare maza ba shi da ruwan famfo, sannan ban ɗakinsa ba ya aiki.
Azabar da wadanda aka kama suka sha a NSCDC
Waɗanda suka tsira sun shaida cewa sun fuskanci tsananin zafi, ƙarancin ruwa a jikinsu da kuma mummunan cunkoso.
Munin lamari har ya kai ga mutane ba su iya motsi yadda ya kamata a ɗakin da girmansa bai wuce murabba'in mita 12 ba.
Kwamitin mai mambobi 10, wanda Jonathan Kure ya jagoranta, ya tabbatar da mutuwar mutane 33 a hannun hukuma.
Hakan ya faru ne tsakanin 8:00 na dare ranar 16 ga Satumba 2026 zuwa ƙarfe 7:00 na safe ranar 17 ga watan Satumba 2026.
Kananan yara da mata sun ci bakar wahala
Daga binciken aka gano mutum 14 cikin waɗanda suka mutu yara ne. Duk da ƙananan yara ne, an ajiye su ne a dakin manya.
A wurin mata ma haka abin yake, an ce babu ruwan sha kuma kewayen bai aiki. da kyau.
Rahoton ya bayyana mummunan yanayin da ake tsare da wadanda aka kama, aka ce mutum 41 G suka tsira daga lamarin.
Ya gano cewa an kulle kusan maza 50, ciki har da ƙananan yaran a cikin ɗaki mara iska mai dauke da ƙaƙƙarfan ƙofar ƙarfe.
Cunkoso, ƙishi da yunwa ya kashe mutane
Kwamitin ya ce jami’an da ke kula da ɗakin sun gaza rage cunkoson, duk da koke-koken masu haƙar ma’adanan da aka kama.
Sun yi ta bugun ƙofa da bango da suke neman taimako. Haka kuma, ba jami’an tsaron ba su samar masu da agajin gaggawa ba.
Bayan nan, kwamitin ya kuma ce an hana 'yan uwan fursunonin kai musu abinci a ranar Laraba, 16 ga Satumba 2026.
Tun misalin ƙarfe 7:15 na yammacin ranar, mutanen suka fara nuna alamun matsalar lafiya, ciki har da kaikayin idanu.
Sun yi kukan jin zafi a maƙogwaro, wahalar numfashi, zufa mai yawa da tsananin ƙishirwa, amma haka aka yi biris da su.
Daga bisani, sun fara ihun neman taimako tare da roƙon ruwa cikin dare amma manyan jami’ai suka hana a kula da su.
Ko da suka daina ihu, ba a bari an bude wadannan mutane ba, zuwa washegari da safe da aka bude su kuwa sai dai aka ga gawa.

Source: Getty Images
NSCDC: Kwamiti ya bukaci a biya dangin mamata diyya
Rahoton nan cewa yake yi kwamitin bincike ya bukaci a biya Naira biliyan 1.4 a matsayin diyya ga iyalan mutum 33 da suka mutu a hannun NSCDC a Neja.
Ya kuma bukaci a biya sauran wadanda suka tsira da rai, sannan a sallami kwamandan NSCDC na jihar tare da gurfanar da jami’an da ke da hannu a lamarin.
Ministan harkokin cikin gida, Tunji-Ojo, ya yi alkawarin aiwatar da shawarwarin domin tabbatar da adalci.
Asali: Legit.ng


