Sheikh Gumi Ya Shiga Maganar Sanata Shehu Buba da Ake Zargi da Ta’addanci

Sheikh Gumi Ya Shiga Maganar Sanata Shehu Buba da Ake Zargi da Ta’addanci

  • Shiekh Ahmad Abubaar Mahmud Gumi ya tsoma baki kan zargin Sanata Shehu Buba daga jihar Bauchi kan alaka da ta'addanci
  • Malamin ya yi kira da a guji bita da kullin siyasa a matsayinsa na wanda ya ba da gudunmawa sosai wurin tabbatar da tsaro
  • Ya ce Sanata Shehu Buba ya daɗe yana tallafa wa jami’an tsaro wajen yaƙi da rashin tsaro a matsayin farar hula

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Babban malamin Musulunci a Kaduna, Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya yi magana kan zargin Sanata Shehu Buba da ake yi.

Malamin ya bayyana irin gudunmawar da sanatan ya bayar wurin tabbatar da kawo karshen matsalolin tsaro da ke damun al'umma.

Gumi ya bukaci adalci kan zargin Shehu Buba da ta'addanci
Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi da Sanata Shehu Buba. Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, Mujaddadi TV.
Source: Facebook

Sheikh Gumi ya bayyana haka ne a cikin wani rubutu da ya yi a Facebook yammacin Lahadi 13 ga watan Satumbar shekarar 2026.

Kara karanta wannan

Bata sunan OPay: Bashir Ahmad ya roki alfarma kan cafke Hafsat

Sheikh Gumi ya fadi ƙoƙarin Sanata Shehu Buba

Malamin ya ce a matsayinsa farar hula, Sanata Shehu Buba ya kasance yana tallafa wa ƙoƙarin jami’an tsaro wajen yaƙi da ’yan bindiga da sauran matsalolin tsaro.

Ya ce ya kamata a yi binciki sanatan cikin adalci da gaskiya, ba tare da karkatar da ayyukansa saboda bambancin siyasa ba.

Gumi ya ce bambancin ra’ayin siyasa halas ne, amma da gangan ɓata sunan mutumin da ya bayar da gudunmawa wajen yaƙi da rashin tsaro rashin adalci ne.

Shehin malamin ya ce yin hakan domin samun wata fa’ida ta siyasa ba shi da kyau, kuma hakan na nuna rashin sanin ya kamata.

Zargin Shehu Buba da ta'addanci na sauya salo
Sanata Shehu Buba da ake zargi yana da alaƙa da ta'addanci. Hoto: Mujaddadi TV.
Source: Facebook

Gumi ya bukaci yi wa Shehu Buba adalci

Ya ƙara da cewa idan har ba za a yaba da ƙoƙarin Sanata Shehu Buba ba, to bai kamata a karkatar da gaskiyar ayyukansa ba.

Ya rubuta cewa:

"Bai kamata a mayar da zargin mai girma Sanata Shehu Buba Umar wata bita da kullin siyasa ba, a matsayinsa na farar hula, ya kasance yana tallafa wa ƙoƙarin jami’an tsaro wajen yaƙi da ’yan bindiga, don haka ya cancanci a yi masa adalci da kuma tantance ayyukansa cikin gaskiya da haƙiƙa.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An ɗauko abin da ya faru a mulkin Buhari fiye da shekara 1 bayan ya bar duniya

"Bambancin ra’ayin siyasa abu ne da ya halatta, amma yin ƙoƙarin ɓata sunan mutumin da ya bayar da gudunmawa wajen yaƙi da rashin tsaro domin cimma wata manufa ta siyasa, rashin adalci ne kuma abin zargi.
"Idan ba za ku yaba da ƙoƙarinsa ba, aƙalla ka da ku karkatar da gaskiyar abin da ya yi domin amfanin siyasa."

Zargin ta'addanci: PRP ta kare Shehu Buba

Mun ba ku labarin cewa jam’iyyar PRP ta kare Sanata Shehu Buba kan zargin alakarsa da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

PRP ta ce ta tabbatar zarge-zargen wani shiri ne na bata sunan ɗan takararta gabanin zaɓen 2027, saboda karuwar farin jininsa.

Jam’iyyar ta yi barazanar daukar matakin shari’a, tana mai cewa dokar zaɓe ta 2026 ta tanadi hukunci kan yada bayanan ƙarya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.